Ministan muhalli, Mista Balarabe Lawal, ya nuna damuwarsa kan yanayin kwararowar hamada da zaizaiyar kasa da ake fama da su, yana mai cewa suna barazana ga rayukan ‘yan Nijeriya sama da mutum miliyan 40, kuma tuni matsalar ta shafi kaso 43 na filin kasar nan, wanda aka yi kiyasin murabba’in kilomita 923,000.
Lawal ya shaida hakan ne a lokacin yake jawabi a Abuja yayin wani babban taro mai taken ‘dawo da fili da kuma bude wasu sabbin damarmaki’, wanda cibiyar bunkasa aikin jarida ta CJID ta shirya a karkashin shirinta kan dumamar yanayi, tare da tallafin ma’aikatar muhalli ta tarayya.
- Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
- Alakar Sin Da EU Na Bukatar Hadin Gwiwa Ba Raba-gari Ba
Da yake samun wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Dakta Mahmud Kambari, ministan ya misalta zaizaiyar kasa da hamada matsayin babban matsala da ke shafan duniya baki daya.
Lawal ya yi nuni da cewa, gurbacewar fili ya haifar da asarar ton biliyan 24 na fadin kasa mai albarka a duniya, abin da ya janyo rage yawan samar da abinci tare da yin barazana ga samar da abinci mai wadata.
Da yake buga hujja da shirin yaki da kwararowar hamada na Majalisar Dinkin Duniya (UNCCD), Lawal ya ce sama da hekta miliyan 2 ake asararsu duk shekara sakamakon kwararowar hamada, gurbacewar kasa da kuma fari.
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli.
A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi.
Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba.
Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka, shirye-shirye, ayyukan da ke da nufin magance gurbacewar kasa, kwararowar hamada, da barazanar muhalli masu alaka.
Tun da farko, babban manajan shirye-shirye a CJID, Mista Ifeanyi Chukwudi ya shaida cewa cibiyar na aikin hadin guiwa da ma’aikatun da abun ya shafa da masu ruwa da tsaki wajen inganta hanyoyin kare muhalli da dakile zaizaiyar kasa ko hamada.
Ya kara da cewa CJID na kuma taimaka wa wajen zurfafa bincike da kara samar da wayar da kai ga jama’a daga wajen ‘yan jarida kan yadda za a tunkarar manyan matsalolin kwararowar hamada, gurbacewar kasa da kuma fari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp