Rahoton bankin duniya na shekara 2022 ya nuna cewa ‘yan Nijeriya miliyan 70 ba sa iya samun taftataccen ruwan da za su sha, sannan miliyan 114 ba sa iya samun kayayyakin tsaftar muhalli a 2021.
Rahoton mai taken ‘samar da ruwan sha a duniya da tsaftar muhalli’ ya nuna kashi 36 ne ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a 1990, yayin da aka samu kasha 11 a 2021.
- Zaben Kananan Hukumomin Osun Haramtacce Ne – Kotu
- Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Zai Dawo Aikin Jigilar Fasinjojinsa Ranar Litinin Mai Zuwa
A cewar rahoton, “A 2021, ‘yan Nijeriya miliyan 70 ne ba sa iya samun tsaftatccen ruwan sha, sannan miliyan 114 ba sa iya samun kayayyakin tsaftace muhalli. An samu kashi 36 ne ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a 1990, yayin da aka samu kashi 11 a 2021. Kididdiga ya nuna cewa kashi 19 na ‘yan Nijeriya ba a kula da su a 2020, sanna ba sa iya samun halin tsaftace muhalli.
“A 2016, an samu adadin yawan mutane da suka kai kusan kashi uku suna amfani da hanyoyin samun ruwa wadanda suka gurbata wanda hakan na iya shafar lafi-yarsu.”
Haka kuma rahoton ya bayyana cewa akwai bukatar tallafa wa gwamnati wajen kokarin sake gina inganta harkokin mulki.
Da yake yin jawabi kan rahoton, Farfesa a bangaren harkokin lafiya, Tanimola Akande ya bayyana cewa wannan ba karamin abun takaici ba ne kan matsalar samun tsaftataccen ruwan sha a Nijeriya.
“Dole ne a samar wa mutane tsaftataccen ruwan sha wajen gudanar da harkokin gida da samun lafiya da ake bukata.
“Gurbataccen ruwan sha yana janyo cututtuka masu yawan gaske, wanda hakan ne ya sa ake samun yawan cutuka a Nijeriya. Sannan yana iya janyo mutuwar mu-tane masu yawa.
“Domin bunkasar lamarin, kowa yana da irin rawar da zai iya takawa. A matakin gida, ya kamata mutane su yi kokarin samar da ruwa mai tsafta da hanyoyin samun ruwa masu inganci domin samun lafiya,” in ji Akande.