• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Ganin Tasku Kan Tsadar Kayan Abinci

by Abubakar Abba
2 years ago
Abinci

A cikin ‘yan makwannin da suka gabata, ‘yan Nijeriya sun damu a cikin halin da suka tsinci kansu na ci gaba da fuskantar hauhawan farashin kayan abinci.

Hukumar kdiddiga ta kasa ta NBS ta bayyana cewa, hauhawan farashin kayan abinci daga shekara zuwa shekara, haka farashin man girki Burondi, hatsi, Tumatir, Doya, Kifi, Nama kayan lambu da sauransu, duk sun yi tashin gwaron Zabi.

  • Tsohon Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Gidan Rediyon Kano
  • Kiwon Lafiya: Yadda Dabi’un Ko-in-kula Ke Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke

Acewar hukumar ta NBS,  hauhawan farashin na kayan abinci, ya karu da kashi  22.22 a cikin dari a cikin watan Afirilun 2023.

A bisa jin farashin kayan abinci da aka yi a wasu kasuwannin kasar nan,  a watan Yulin 2023, farashin ya nuna cewa, farashin Kwandon Tumatir daya, ya kai daga Naira   90,000 zuwa Naira 100,000, sabanin yadda a baya, ake sayar da Kwandon sa daya akan Naira 20,000.

Har ila yau, farashin Kwandon Tattasai wanda a baya ake sayar wa daga akan Naira 12,000 zuwa Naira 15,000,a yanzu ana sayar da Kwandon sa daya daga Naira   40,000 zuwa Naira 45,000.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Sauran kayan abincin kamar su, Taliyar Golden Penny Pasta ta Leda mai dauke da guda 20 duk katan daya ana sayar da shi kan Naira 10,200, haka Taliyar  Chicken Flabour Instant Noodles mai dauke da guda 40 a cikin Leda, ana sayar da duk katan daya kan Naira 8,000 samarin Knorr Chicken Maggi duk katan daya ana sayar da shi kan Naira 21,000.

Baya ga hauhawan farashin kayan abincin da ake ci gaba da fuskanta, an kuma danganta tashin gwaron Zabin kayan abincin akan tsadar farashin man fetur da rabar da shi da faduwar darajar Naira da kuma karancin kayan aikin gona.

Wadannan matsalolin da aka zayyano, kari da kalubalen rashin tsaro a kasar nan sun kara jefa, musamman talakawan kasar nan a cikin halin kuncin rayuwa.

A daya bangaren, wasu daga cikin manoman kasar nan, na ci gaba da fuskantar tsadar farashin kayan aikin noma, mussaman saboda tsadar farashin takin zamani da magungunan kashe kwari da rashin samun ingantaccen Irin noma da kuma rashin samar masu da kyayawan tsari, don yin noman rani.

Wani magidanci dan shekara 47 mai suna Emmanuel Ikechukwu da ke da zama a anguwar Orozo da ke Abuja wanda kuma yake da iyalai 6 ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya taba fuskantar matsin ruyuwa da ta hade masa da hauhawan farashin kayan abinci da tsadar sufuri.

A cewar Ikechukwu,“ Komai ya yi tsada a kasuwa har naji ba zan iya jurewa wa da hakan ba, ba a yi wani karin albashi ba amma farashin komai ya tashi. “

“Wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya taba fuskantar matsin ruyuwa da ta hade masa da hauhawan farashin kayan abinci da tsadar sufuri. “

Ya ce, me ya sa gwamnati ke kirkiro da tsare-tsaren da suke jefa rayuwar talakawan kasar nan a cikin halin kuncin rayuwar kuma shin, muna da sauran wata fata a Nijeriya kuwa  ?.

Wasu magidantan na ta hakilon samar wa iyalansu abinda za su ci, amma farashin kayan abincin, sai kara hauhawa yake yi.

Wasu gidajen da dama, sun rage yawan kayan abincin da  suke sayawa  ahalinsu, haka sun dakatar da sayen manya kayan more rayuwa da suka saba sayawa ahalansu.

Wani malamin makaranta mai suna Mallam Abubakar Usman wanda ke da zama a yankin Karu  a Abuja, shi ma kokawa ya yi akan hauhawan farashin kayan abincin.

Abubakar ya ce, a yanzu haka ni da dan uwa na, muna tsallake cin abinci har da ‘ya’yana uku saboda tashin gwaron Zabin na kayan masarufin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Xi Jinping: Zurfafa Gyare-gyare A Cikin Jam’iyya Da Hukumomin Gwamnati, Muhimmin Mataki Ne Na Zamanintar Da Karfin Tafiyar Da Harkokin Mulki

Xi Jinping: Zurfafa Gyare-gyare A Cikin Jam'iyya Da Hukumomin Gwamnati, Muhimmin Mataki Ne Na Zamanintar Da Karfin Tafiyar Da Harkokin Mulki

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.