Wani sabon bincike da cibiyar kididdigar ayyukan ta’addanci ‘Crime Experience and Security Perception Survey’ (CESPS) da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta gudanar ya nuna cewa ‘yan Nijeriya sun biya Naira Tiriliyan 2.23 a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutane tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
Rahoton ya nuna yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a fadin kasar da kuma mawuyacin hali da iyalai ke shiga.
- Nijeriya Da Brazil Sun Cimma Yarjejeniyar Bunkasa Noman Zamani A Kasar Nan
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Ga Matakin EU Na Sanya Takunkumi Kan Kamfanonin Kasar Sin
A cewar binciken, kashi 65 cikin 100 na iyalai da aka yi garkuwa da su, an tilasta musu biyan kudin fansa domin a sako ‘yan uwansu. Matsakaicin kudin fansa da aka biya ya kai Naira miliyan 2.67, wanda ya nuna halin kunci da nauyi da aka dora wa wadanda abin ya shafa.
CESPS ta tabbatar da cewa, an tafka ayyukan ta’addanci miliyan 51.89 da ya shafi iyalai a Nijeriya a cikin watanni 12. Yankin Arewa-maso-Yamma ya zama yankin da lamarin ya fi kamari, inda aka bayar da rahoton laifuka miliyan 14.4, sai kuma Arewa ta Tsakiya mai laifuka miliyan 8.8. Yankin Kudu-maso-Gabas shi ke da mafi ƙarancin adadin laifukan da aka tafka, inda yake da akalla miliyan 6.18.
Binciken ya ci gaba da nuna cewa, yawan laifukan ya fi yawa a yankunan karkara fiye da na birane.
Yawancin wadanda abin ya shafa, sun yi imanin cewa, sanar wa hukumar ‘yansanda domin kubutar da iyalansu a wurin masu garkuwar bai cika haifar da wani mataki mai ma’ana ba.