‘Yan Nijeriya da dama sun jingine harkokin kasuwancinsu a jihar Agadas ta Jamhuriya Nijar, inda suka shiga halin damuwa tun bayan da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya kara jaddada matakinsa na sabunta takardun kudi na Naira daga nan zuwa 10 ga watan Fabarairu 2023.
Da yawa sun gwammace jingine harkar kasuwancin da suke yi tsakanin Nijar da Nijeriya saboda karancin sabbin takardun kudin yayin da magidanta daga cikinsu, suka ce sun kasa aik ewa iyalansu da kudi gida.
- Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Kamo Mata Shugaban Jam’iyyar APC Na Kano Abdullahi Abbas
- Wakilin Sin Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Ministan Wajen Gabon
Sai dai bayan korafe-korafe da jama suka dinga yi a yau Litinin, CBN ya bai wa bankuna umarnin bai wa Kwastomomi sabbin kudi a kan kanta.
Kafin wannan umarni na CBN mutane na ci gaba da fuskantar kalubale na karancin kudin, lamarin sa ya haifar sa tsaiko ga kasuwanci.