Jam’iyyar PDP ta ce ’yan Nijeriya za su kayar da jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda ’yan Ghana suka yi wa jam’iyyar NPP a zaben da aka kammala a kasar.
Hukumar zabe ta Ghana ta ayyana John Mahama na jam’iyyar NDC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
- Firaministan Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Tare Da Shugabannin Muhimman Kungiyoyin Tattalin Arzikin Kasa Da Kasa
- Jami’ar Kwara Ta Rage Wa Masu Bukata Ta Musamman Kudin Karatu
Mahama, wanda ya taba zama shugaban kasa daga 2012 zuwa 2017, ya doke dan takarar jam’iyyar mai mulki, Mahamudu Bawumia, inda ya samu kashi 56.5 na kuri’un da aka kada.
Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya ce nasarar Mahama ta nuna karfin ikon jama’a kan mulkin danniya.
Ya soki APC saboda manufofin da suka jefa ’yan Nijeriya cikin talauci, inda ya bayyana cewa za su kayar da APC a 2027 don dawo da shugabanci nagari da kwanciyar hankali a kasa a karkashin PDP.
Ologunagba, ya kuma zargi shugabannin APC da yin buris da halin da talakawa ke ciki.
Ya kara da cewar sun mayar da hankali kan yin rayuwa cikin jin dadi, suna kashe arzikin kasa ba tare da kulawa ba, lamarin da ya kara tabarbarewar tattalin arziki, tsaro, da ingantaccen rayuwa a Nijeriya.