Shugaban rundunar tsaron sa-kai na Jihar Sakkwato, Yusha’u Kebbe, ya ce rundunar za ta taka muhimmiyar rawa a wajen dakile ayyukan ta’addanci a Arewa Maso Yammacin Nijeriya tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro.
Kebbe, ya bayyana hakan a yayin tataunawarsa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN).
- Matatar Dangote Ta Karbi Danyen Mai Karo Na 4 Daga NNPCÂ
- Matatar Dangote Ta Karbi Danyen Mai Karo Na 4 Daga NNPCÂ
Ya ce an samar da rundunar ne da zummar dawo da zaman lafiya a yankunan Jihar Sakkwato da ke fama da matsanancin matsalar tsaro.
Ya ce a rukunin farko sun debi mutane 2000 da ‘yansanda da rundunar soji za su bai wa horon na musamman kan dabarun yaki.
“Horon zai dauki tsawon watanni biyu, a horon za a koyar da su yadda za su yi amfani da makamai da tattara bayanai da kuma yadda za su kare kansu daga fadawa cikin hatsari” in ji shi.
Kebbe, ya ce dukkanin makaman da rundunar za ta yi amfani da su, za su zama a karkashin kulawar rundundar ‘yansandan kowace karamar hukuma a jihar.