‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 na kasar Sin dake aiki a tashar binciken samaniya ta kasar, sun kammala jerin ayyuka karo na uku a wajen kumbonsu a jiya Juma’a.
A cewar hukumar kula da ayyukan ‘yan sama jannati ta Sin ko CMSA, ‘yan sama jannatin Chen Dong, da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun yi ayyuka na tsawon sa’o’i shida da rabi, tare da kammala ayyuka masu nasaba, da misalin karfe 11 saura mintuna 13 na dare bisa agogon Beijing, inda suka samu tallafi daga hannun mutum-mutumin inji na tashar samaniyar, da kuma tawagar masu sarrafa na’urori dake doron duniya.
Yayin da suke gudanar da ayyukan, Chen Dong da Wang Jie dake aikin tattaki a wajen tashar, sun kammala harhada na’urorin kawar da birbishin abubuwan dake wajen tashar, da kayayyakin dake taimakawa na’urar sufuri dake kewayawa a wajen tashar, kana sun duba tare da gyara dukkanin kayayyakin aiki dake wajen tashar.
Ya zuwa yanzu, Chen Dong, ya kammala zagaye shida na ayyukan tattaki a wajen tashar ta samaniya, inda ya zamo dan sama jannatin kasar Sin mafi shafe tsawon lokaci yana tattaki a wajen tashar sararin samaniya ta Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp