Rundunar ‘yan sandan Jihar Ebonyi ta kama wani Mista Enyi Friday da ake zargin dan sandan bogi ne a jihar.
Kakakin rundunar, SP Chris Anyanwu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abakaliki, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar.
- Gwamnatin Zamfara Ta Fara Horas Da ‘Yan Sa-Kai Don Yakar ‘Yan Bindiga
- Cutar Amai Da Gudawa Ta Bulla A Kano
“Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi a ranar Asabar 3 ga watan Yuli, ta hanyar hadin gwiwa tare da Anyigor Lazarus, Kwamandan jami’an tsaro na Ebubeagu da ke karamar hukumar Ezza ta kudu, sun kama Enyi a ranar Juma’a.
“Wanda ake zargin wanda ya fito daga unguwar Umunwagu Idembia da ke yankin, ya yi shi jami’in ‘yan sanda ne.
“Saurayin wanda ba dan sanda ba ne, an kama shi sanye da kayan Kofur na ‘yan sanda, don haka aka kama shi.
Anyanwu ya bayyana cewa, “An mika shi ga sashen binciken leken asiri na jihar, domin gudanar da bincike”.
Kakakin ya bukaci jama’a da su ci gaba da hada kai da ‘yan sanda a jihar, domin kawar da al’umma daga masu aikata laifuka.