Masu iya magana sun ce ‘Idan maciji ya sari mutum da zarar ya ga tsumma sai ya yi tsammanin wani ne zai kara saransa wannan al’amarin haka ne yake, zuwa yanzu dai abin da ake jira shi ne zaben 2023, an yi zabubbuka samfuri biyu, na shugaban kasa, gwamnoni, majalisun dokoki na tarayya da Jihohi, kai har ma da na ‘yan autan mukaman siyasa wato Kansiloli.
Duk wani abin da dan siyasa yake yi sai ya samu hadin kai na masu yin zabe, da jagororinsu. Akwai masu tunanin watakila an yi karatun ta natsu, sai dai har yanzu abin bai canza zane ba.
- Tsoma Baki Da Lalata Tsarin Samar Da Kayayyaki Da Amurka Ke Yi Bai Samu Karbuwa Ba
- Sin Tana Bayar Da Damar Hadin Gwiwa Ta Hanyar Ayyukan Binciken Duniyar Wata Na Chang’e
Yayin da wasu Kansilolin gwamnonin ne suke dauki dora, wani lokacin ma har da Shugabannin kananan humomin nadi ake yi a wasu Jihohin ba zabe ba, sai dai abinda gwamna ya ga damar yi domin shi ne yake da wuka da nama a hannunsa. .
Halin da ake ciki yanzu ku san fiye da shekara bakwai suna kan karagar mulkin, duk da yake dai ba a taru aka zama daya ba, akwai wadanda sun maida ragon Layyarsu, yayin da wasu kuma har yanzu ana bin su bashi sun kasa maidawa. Idan bera na da sata to ita ma daddawa tana da wari.
Wasu ma ‘yan siyasar bayan zaben nasu wasu ma ba a barin ko nisawa su fara yi, ko rantsar da su ba a yi ba, ko ma kanshin ita majalisar ba su fara ji ba, amma sai ka ga ana ta turereniya wani lokaci wajen zuwa ganinsu.
Wani abu mai daure kai shi ne yadda ranar zabe za ka ga wasu masu kada kuri’a sun sa ganye a kansu, ma’ana wadannan suna nuna cewar su a kasuwa suke, jira kawai suke a taya. Watakila ma shi ya sa Bahaushe yake cewa kowanne Gauta ja ne sai dai idan ba a kai shi rana ba amma a cikin wasan dare, kamar yadda aka ce mugu shi ne wanda ya san makwancin mugu, tamkar dai barawon tsaye ne da na zaune. To da zarar masu sayen kuri’u sun ga irin wadannan masu son sayar da katin zabensu abin da aka fi sani da kuri’a, wannan shi ake cewa kaya sun tsinke a gindin kaba.
Ina iya tunawa a shekarar 2015 na je Jihar Zamfara daga sashen Arewa maso yamma na ga irin wannan al’amari wanda ya yi matukar ba ni mamaki, saboda yadda masu aikata wannan al’amari na sayen kuri’a da masu sayarwa a wata mazabar da ba ta da nisa da Unguwar Zabarmawa a Gusau babban birnin Jihar suka ci karensu babu babbaka. Wani al’amari kuma mai daure kai da ban al’ajabi shi ne lokacin da ake al’adar nan ta tantancewa, wani lokacin a cikin gidan mutum za a shiga a yi mashi cin mutunci da sunan tantancewa.
A gabana na ga yadda aka fara zabga wa wani matashi bulala da sunan tantancewa kamar wadanda da ma akwai jikakka tsakaninsu. Ana yin magana ai wane ba rago ba ne zai iya shanyewa har sai da ta kai ga ba ya iya jurewa, da ya ga abin ba zai iya jurewa ba sai ya ranta a na kare. Duk irin wannan ai ‘yan barandar wasu ‘yan siyasa ne suka aiwatar da ita mummunar al’adar ta tantancewa, da ma masu iya magana sun ce kowa ya samu rana sai ya yi shanya.
A wancan lokacin da yake talauci bai kai tsananin na yanzun ba, abin da na gane wa idanuna a wata mazaba, na ga masu sayen kurui’u, tare da masu sayarwa. Abin na nuna kowa ya san kowa, suna zuwa sai ya amshi kuri’ar ya ba su dan abinda bai taka kara ya karya ba, domin bai wuce Naira 200 ba, har wata da ta bayar da kuri’arta, aka ba ta abin hasafin nata, har ma magana take cewa yau ta samu abin yin jar miya. Wannan duk ya faru ne a gaban jam’an tsaro wadanda su dama aikinsu shi ne idan sun ga irin haka su yi saurin daukar mataki, amma ina shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.
Idan har irin wannan abin takaicin zai iya faruwa a babban birnin Jiha ko na ce hedikwatar Jiha a ranar da ake zabe, me zai iya faruwa ke nan a kauyuka wuraren da ba kasafai ake samun isassun jami’an tsaro ba?
Sai kuma wata karamar hukuma a Arewa da wani al’amari ya kai ni can inda na ga wani abin da ya kara ba ni mamaki da ya fi wanda na gani da farko, domin kuwa irin ‘yan siyasar da ake kira ‘yan goma-goma irin na mazabun Kansila. Bayan sun ci abincin rana a sakatariyar karamar hukumar sai ka ga mutum yana sosa keya, kamar yaron da ya aikata laifi aka kama shi, abin da za ka ji ya ambata a matsayin bankwana sai ya ce wallahi yau ban da kudin cefane, ko zai yi ma ‘yarsa aure, kai da dai sauran abubuwan da ba su kamata ba a ce ana fada wa masu mukaman siyasa.
Dukkan wadanda suka yi bankwana da shugaban karamar hukumar babu mutumin da ya yi maganar a unguwarsu suna bukatar a zo a yi masu aikin da zai bunkasa wurin nasu. Kowa bukatar kansa yake gabatarwa kamar dai yadda na ji da kunnena, don haka a irin wannan yanayin ne har za a yi maganar wani ci gaban al’umma, ni a nawa ganin abin ai zai yi matukar wuya.
Ba abin mamaki ba ne ganin yadda wasu mutane za su yi tafiyayya daga garuruwansu babu kuma inda za su yi birki sai Majalisar Wakilai, ko ta Dattawa haka abin yake har zuwa na Jihohi duk dai Kanwar ja ce. Ko a same su a ofis ko a je gidajensu, duk dai bukatun na mutane ne inda kowa yake bayyana nasa.
Wani lokaci ma sai su manta da kwatancen hanyar da za su bi zuwa gidan sai sun tambaya, da gangan ne ma har ka saurari mutane suna maganar cewa babu wasu ayyukan da aka yi masu wadanda za su kawo masu ci gaba. Ai abin yana da kamar wuya Gurguwa da auren nesa, saboda dama in har an hau motar kwadayi to dole a sauka a tsashar wulakanci.
Akwai mutanen mazabun da suke bibiyar ayyukan da za a yi masu na mazabu, da kudaden da aka ware, da kuma lokacin da za a fara yin su ayyukan. Ta daya bangarensu ba a yi ayyukan da mutanensu za su amfana ba, tambaya suke yaushe ne dan majalisar nasu zai zo ne, domin su je su bayyana ma shi nasu bukatunsu.
Ba ana nufi babu masu bibiyar lokacin da ake ba da kudaden yi wa mazabu aiki ba ne a Arewa domin ai ba a rasa nono a ruga, amma ba su kai yawan sashen kudancin Nijeriya ba. Abubuwan cin fuska da wasu ‘yan majalisun Arewa ke yi wa mazabunsu, idan Kudanci ne ba yadda za su ko ma ko mafarki yin hakan, saboda sun san kwanan wasan.
Da yake tuni suka tsaga suka ga jinni, sun san duk yadda za su tafiyar da mutanen nasu, musamman ma idan sun lura su ba wata maganar ci gaban al’ummarsu ne ya dame su, ashe dama wasu daga cikinsu bukatarsu aljihunsu.
Muddin dai wasu mutane suka nuna kwadayin sai sun samu abin yin hidima, lalle za a dade ana cin tuwon shekaranjiya da miyar wata daya. Shi ya sa ake kallon tsakanin `Yan Siyasa Da Masu Zabe Wane Gautan Ne Ba Ja Ba?