• Leadership Hausa
Monday, January 30, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Bakon Marubuci

‘Yan Siyasa Da Masu Zabe: Wane Gauta Ne Ba Ja Ba?

by Idris Aliyu Daudawa
2 months ago
in Bakon Marubuci
0
‘Yan Siyasa Da Masu Zabe: Wane Gauta Ne Ba Ja Ba?

Masu iya magana sun ce ‘Idan maciji ya sari mutum da zarar ya ga tsumma sai ya yi tsammanin wani ne zai kara saransa wannan al’amarin haka ne yake, zuwa yanzu dai abin da ake jira shi ne zaben 2023, an yi zabubbuka samfuri biyu, na shugaban kasa, gwamnoni, majalisun dokoki na tarayya da Jihohi, kai har ma da na ‘yan autan mukaman siyasa wato Kansiloli.

Duk wani abin da dan siyasa yake yi sai ya samu hadin kai na masu yin zabe, da jagororinsu. Akwai masu tunanin watakila an yi karatun ta natsu, sai dai har yanzu abin bai canza zane ba.

  • Tsoma Baki Da Lalata Tsarin Samar Da Kayayyaki Da Amurka Ke Yi Bai Samu Karbuwa Ba
  • Sin Tana Bayar Da Damar Hadin Gwiwa Ta Hanyar Ayyukan Binciken Duniyar Wata Na Chang’e

Yayin da wasu Kansilolin gwamnonin ne suke dauki dora, wani lokacin ma har da Shugabannin kananan humomin nadi ake yi a wasu Jihohin ba zabe ba, sai dai abinda gwamna ya ga damar yi domin shi ne yake da  wuka da nama a hannunsa. .

Halin da  ake ciki yanzu ku san fiye da shekara bakwai suna kan karagar mulkin, duk da yake dai ba a taru aka zama daya ba, akwai wadanda sun maida ragon Layyarsu, yayin da wasu kuma har yanzu ana bin su bashi sun kasa maidawa. Idan bera na da sata to ita ma daddawa tana da wari.

Wasu ma ‘yan siyasar bayan zaben nasu wasu ma ba a barin ko nisawa su fara yi, ko rantsar da su ba a yi ba, ko ma kanshin ita majalisar ba su fara ji ba, amma sai ka ga ana ta turereniya wani lokaci wajen zuwa ganinsu.

Labarai Masu Nasaba

Yarfe Da Kazafi Tsakanin Manyan ‘Yan Takarar Shugabancin Nijeriya: Duk Gautar Ja Ce?

Ya Wajaba INEC Ta Hana Yakin Neman Zabe Bisa Amfani Da Addini

Wani abu mai daure kai shi ne yadda ranar zabe za ka ga wasu masu kada kuri’a sun sa ganye a kansu, ma’ana wadannan suna nuna cewar su a kasuwa suke, jira kawai suke a taya. Watakila ma shi ya sa Bahaushe yake cewa kowanne Gauta ja ne sai dai idan ba a kai shi rana ba amma  a cikin wasan dare, kamar yadda aka ce mugu shi ne wanda ya san makwancin mugu, tamkar dai barawon  tsaye ne da na zaune. To da zarar masu sayen kuri’u sun ga irin wadannan masu son sayar da katin zabensu abin da aka fi sani da kuri’a, wannan shi ake cewa kaya sun tsinke a gindin kaba.

Ina iya tunawa a shekarar 2015 na je Jihar Zamfara daga sashen Arewa maso yamma na ga irin wannan al’amari wanda ya yi matukar ba ni mamaki, saboda yadda masu aikata wannan al’amari na sayen kuri’a da masu sayarwa a wata mazabar da ba ta da nisa da Unguwar Zabarmawa a Gusau babban birnin Jihar suka ci karensu babu babbaka. Wani al’amari kuma mai daure kai da ban al’ajabi shi ne lokacin da ake al’adar nan ta tantancewa, wani lokacin a cikin gidan mutum za a shiga a yi mashi cin mutunci da sunan tantancewa.

A gabana na ga yadda aka fara zabga wa wani matashi bulala da sunan tantancewa kamar wadanda da ma akwai jikakka tsakaninsu. Ana yin magana ai wane ba rago ba ne zai iya shanyewa har sai da ta kai ga ba ya iya jurewa, da ya ga abin ba zai iya jurewa ba sai ya ranta a na kare. Duk irin wannan ai ‘yan barandar wasu ‘yan siyasa ne suka aiwatar da ita mummunar al’adar ta  tantancewa, da ma masu iya magana sun ce kowa ya samu rana sai ya yi shanya.

A wancan lokacin da yake talauci bai kai tsananin na yanzun ba, abin da na gane wa idanuna a wata mazaba, na ga masu sayen kurui’u, tare da masu sayarwa. Abin na nuna kowa ya san kowa, suna zuwa sai ya amshi kuri’ar ya ba su dan abinda bai taka kara ya karya ba, domin bai wuce Naira 200 ba, har wata da ta bayar da kuri’arta, aka ba ta abin hasafin nata, har ma magana take cewa yau ta samu abin yin jar miya. Wannan duk ya faru ne a gaban jam’an tsaro wadanda su dama aikinsu shi ne idan sun ga irin haka su yi saurin daukar mataki, amma ina shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

Idan har irin wannan abin takaicin zai iya faruwa a babban birnin Jiha ko na ce hedikwatar Jiha a ranar da ake zabe, me zai iya faruwa ke nan a kauyuka wuraren da ba kasafai ake samun isassun jami’an tsaro ba?

Sai kuma wata karamar hukuma a Arewa da wani al’amari ya kai ni can inda na ga wani abin da ya kara ba ni mamaki da ya fi wanda na gani da farko, domin kuwa irin ‘yan siyasar da ake kira ‘yan goma-goma irin na mazabun Kansila. Bayan sun ci abincin rana a sakatariyar karamar hukumar sai ka ga mutum yana sosa keya, kamar yaron da ya aikata laifi aka kama shi, abin da za ka ji ya ambata a matsayin bankwana sai ya ce wallahi yau ban da kudin cefane, ko zai yi ma ‘yarsa aure, kai da dai sauran abubuwan da ba su kamata ba a ce ana fada wa masu mukaman siyasa.

Dukkan wadanda suka yi bankwana da shugaban karamar hukumar babu mutumin da ya yi maganar a unguwarsu suna bukatar a zo a yi masu aikin da zai bunkasa wurin nasu. Kowa bukatar kansa yake gabatarwa kamar dai yadda na ji da kunnena, don haka a irin wannan yanayin ne har za a yi maganar wani ci gaban al’umma, ni a nawa ganin abin ai zai yi matukar wuya.

Ba abin mamaki ba ne ganin yadda wasu mutane za su yi tafiyayya daga garuruwansu babu kuma inda za su yi birki sai Majalisar Wakilai, ko ta Dattawa haka abin yake har zuwa na Jihohi duk dai Kanwar ja ce. Ko a same su a ofis ko a je gidajensu, duk dai bukatun na mutane ne inda kowa yake bayyana nasa.

Wani lokaci ma sai su manta da kwatancen hanyar da za su bi zuwa gidan sai sun tambaya, da gangan ne ma har ka saurari mutane suna maganar cewa babu wasu ayyukan da aka yi masu wadanda za su kawo masu ci gaba. Ai abin yana da  kamar wuya Gurguwa da auren nesa, saboda dama in har an hau motar kwadayi to dole  a sauka  a tsashar wulakanci.

Akwai mutanen mazabun da suke bibiyar ayyukan da za a yi masu na mazabu, da kudaden da aka ware, da kuma lokacin da za a fara yin su ayyukan. Ta daya bangarensu ba a yi ayyukan da mutanensu za su amfana ba, tambaya suke yaushe ne dan majalisar nasu zai zo ne, domin su je su bayyana ma shi nasu bukatunsu.

Ba ana nufi babu masu bibiyar lokacin da ake ba da kudaden yi wa mazabu aiki ba ne a Arewa domin ai ba a rasa nono a ruga, amma ba su kai yawan sashen kudancin Nijeriya ba. Abubuwan cin fuska da wasu ‘yan majalisun Arewa ke yi wa mazabunsu, idan Kudanci ne ba yadda za su ko ma  ko mafarki yin hakan, saboda sun san kwanan wasan.

Da yake tuni suka tsaga suka ga jinni, sun san duk yadda za su tafiyar da mutanen nasu, musamman ma idan sun lura su ba wata maganar ci gaban al’ummarsu ne ya dame su, ashe dama wasu daga cikinsu bukatarsu aljihunsu.

Muddin dai wasu  mutane suka nuna kwadayin sai sun samu abin yin hidima, lalle za a dade ana cin tuwon shekaranjiya da miyar wata daya. Shi ya sa ake kallon tsakanin `Yan Siyasa Da Masu Zabe Wane Gautan Ne Ba Ja Ba?

Tags: GautaJaSiyasaZabe
Previous Post

Samun Man Fetur Ne Ya Kashe Masa-na’antunmu – Al-Mustapha

Next Post

Sarkin Zazzau Ya Nada Sabon Ardon Zazzau

Related

Yarfe Da Kazafi Tsakanin Manyan ‘Yan Takarar Shugabancin Nijeriya: Duk Gautar Ja Ce?
Bakon Marubuci

Yarfe Da Kazafi Tsakanin Manyan ‘Yan Takarar Shugabancin Nijeriya: Duk Gautar Ja Ce?

2 days ago
Ya Wajaba INEC Ta Hana Yakin Neman Zabe Bisa Amfani Da Addini
Bakon Marubuci

Ya Wajaba INEC Ta Hana Yakin Neman Zabe Bisa Amfani Da Addini

1 week ago
Ko Ayyana Goyon Baya Ga Dan Siyasa Da Wasu Ke Yi Zai Yi Tasiri?
Bakon Marubuci

Ko Ayyana Goyon Baya Ga Dan Siyasa Da Wasu Ke Yi Zai Yi Tasiri?

2 weeks ago
Emefiele: Duk Mai Tunanin Sauro Ya Yi Kadan Bai Kwana Da Shi Ba Ne!
Bakon Marubuci

Emefiele: Duk Mai Tunanin Sauro Ya Yi Kadan Bai Kwana Da Shi Ba Ne!

3 weeks ago
Bukatar Sake Fasalin Yadda Ake Karbar Sabon Katin Zabe
Bakon Marubuci

Bukatar Sake Fasalin Yadda Ake Karbar Sabon Katin Zabe

4 weeks ago
Man Kolmani: Yaushe Za A Fara Cin Moriyarsa?
Bakon Marubuci

Man Kolmani: Yaushe Za A Fara Cin Moriyarsa?

2 months ago
Next Post
Sarkin Zazzau Ya Nada Sabon Ardon Zazzau

Sarkin Zazzau Ya Nada Sabon Ardon Zazzau

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Za Ta Samar Da Karfin Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya A Shekarar 2023

Kasar Sin Za Ta Samar Da Karfin Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya A Shekarar 2023

January 30, 2023
Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Bunkasa Farfadowar Tattalin Arziki Da Daidaito A Fannin Cinikayyar Waje Da Zuba Jari

Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Bunkasa Farfadowar Tattalin Arziki Da Daidaito A Fannin Cinikayyar Waje Da Zuba Jari

January 29, 2023
Buhari Ya Nada Dogara A Matsayin Sabon Darakta Janal Na Hukumar NYSC

Buhari Ya Nada Dogara A Matsayin Sabon Darakta Janal Na Hukumar NYSC

January 29, 2023
Jirgin Sama Kirar Kasar Sin Samfurin C919 Ya Tashi A Karon Farko Cikin Sabuwar Shekarar Zomo

Jirgin Sama Kirar Kasar Sin Samfurin C919 Ya Tashi A Karon Farko Cikin Sabuwar Shekarar Zomo

January 29, 2023
Sin Na Gabatar Da Kyakkyawan Misali A Fannin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa In Ji Wani Masani

Sin Na Gabatar Da Kyakkyawan Misali A Fannin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa In Ji Wani Masani

January 29, 2023
APC Ta Kasa Cika Alƙawarin Sauya Fasalin Ƙasa, In Ji Atiku

APC Ta Kasa Cika Alƙawarin Sauya Fasalin Ƙasa, In Ji Atiku

January 29, 2023
Kwantena Ta Latse Wata Motar Bas, Ta Kashe Fasinjoji 8 A Legas

Kwantena Ta Latse Wata Motar Bas, Ta Kashe Fasinjoji 8 A Legas

January 29, 2023
Abubuwan 5 Da Zaku So Ku Ji A Ganawar Gwamnan CBN Da Shugaba Buhari A Daura

Abubuwan 5 Da Zaku So Ku Ji A Ganawar Gwamnan CBN Da Shugaba Buhari A Daura

January 29, 2023
Inganta Ilimi: Gwamnatin Jihar Gombe Ta Dauki Karin Sabbin Malamai 1,000 Aiki

Inganta Ilimi: Gwamnatin Jihar Gombe Ta Dauki Karin Sabbin Malamai 1,000 Aiki

January 29, 2023
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano Ta Cafke Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano Ta Cafke Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya

January 29, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.