A yayin taron kolin kasashen G7 da aka yi kwanan nan, yunkurin wasu ‘yan siyasar kasar Japan na wanke kasar daga laifin aiwatar da shirin zubar da dagwalon ruwan nukiliya a cikin teku, ya sake gamuwa da cikas. Duba da yadda aka nuna adawa da kakkausar murya, ba’a rubuta “ana maraba da shirin zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku” ba a cikin sanarwar taron kolin, maimakon haka, an ce, ana mara wa hukumar IAEA baya wajen gudanar da bincike cikin ‘yanci.
Ko ma a cikin kungiyar kasashen G7, shirin Japan na zubar da dagwalon ruwan nukiliya a cikin teku ya gamu da ka-ce-na-ce, balle a fadin duniya baki daya. A cikin shekaru biyu, tun daga jama’ar Japan, har zuwa kasashen dake makwabtaka da ita, wato China da Koriya ta Kudu, da tsibaran kasashen yankin tekun Pasific, dukka suna adawa da wannan shirin, inda suka bukaci gwamnatin Japan, da ta dauki matakai ta hanyar da ta dace. A yayin taron kolin kasashen G7 na wannan karo, al’ummun sassa da dama a Japan sun yi zanga-zanga, inda suka soki lamirin gwamnatin kasar suna cewa, zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, babban laifi ne!
A halin yanzu, hukumar IAEA ba ta bullo da rahoton binciken ta na karshe kan shirin Japan na zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku ba, amma gwamnatin Japan ta yi ikirarin cewa, za’a kawo karshen shirin zubar da ruwan kafin karshen watan Yunin bana, kana za’a zubar da ruwan a cikin tekun Pasifik a karshen watan Yuli.
Gaskiya Japan ba za ta iya wanke kanta daga laifin da ta aikata ba, al’amarin da ya shaida rashin daukar nauyi gami da matukar son kai da take nunawa. (Murtala Zhang)