• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Na’urorin Zamani Daidai Lokacin Da Sojoji Ke Da Karancin Makamai -Zulum

by Sani Anwar
5 months ago
Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya koka kan tabarbarewar tsaro a yankin Arewa maso gabas, inda ya bayyana cewa; yanzu haka, ‘yan ta’adda na amfani da fasahohin zamani a kan sojojin Nijeriya.  

A wata hira da aka yi da shi a wani gidan Talajin mai suna ‘News Central TB’ a ranar Laraba, gwamnan ya yi kira da a yi gaggawar shiga tsakani tare da hada hannu tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi, domin kawo karshen tayar da kayar bayan.

  • Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 
  • Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 

Zulum ya bayyana cewa, a halin yanzu; rundunar sojin Nijeriya ba ta da isasshen kayan aikin da za ta iya dakile ci gaba da hare-haren ta’addancin ‘yan ta’adda a yankin ba.

“Sojoji ba su da kayan aikin da ake bukata a kasa, don yakar wadannan ‘yan ta’adda, sannan kuma ina so na sanar da ku cewa; a halin yanzu, maharan na amfani da fasahar zamani wajen yakar sojojin da ke kasa,” in ji Zulum.

Har ila yau, ya bayyana cewa; Babban Hafsan Soji na Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sanar da shi bukatar gaggawar samar da jiragen yaki marasa matuki (UABs), domin bunkasa nasarar yakin.

LABARAI MASU NASABA

Daɓid Adeyemi

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

“’Yan kwanakin da suka gabata, na yi wata ganawa da Babban Hafsan Sojin Kasa, inda ya bay-yana min cewa; yana neman akalla jirage marasa matuka kimanin 32, domin kawo karshen wannan ta’addanci, wanda kuma abin da ya fada din gaskiya ne.

“Kowane jirgi maras matuki, na kai wa kimanin dala miliyan 5.5, don haka, me yasa ba za mu iya hada karfi da karfe wuri guda mu sayi jiragen ba, don bai wa harkar tsaro fifiko?

Har wa yau, ya bayyana kwarin gwiwar cewa; tare da bin tsarin da ya dace da hadin kai a tsa-kanin dukkanin bangarorin gwamnati, za a iya magance wadannan tashin hankula cikin gagga-wa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Labarai

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Next Post
Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

LABARAI MASU NASABA

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.