Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi ikirarin cewa akwai mutanen da ke aiki a matsayin ‘yan leken asiri ga ‘yan ta’adda da suka hada da Sojoji, ‘yan siyasa da sauran mutanen gari.
Da yake jawabi yayin hira da kamfanin labarai na ‘News Central’ a ranar Laraba, gwamnan ya jaddada bukatar sabunta dabarun leken asiri da daukar kwararan matakai don magance matsalar rashin tsaro a yankin.
- Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
- Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna
“Akwai wadanda suka yi hadin gwiwa da ‘yan ta’adda daga cikin sojojin Nijeriya, cikin ‘yan siyasa, da kuma cikin mazauna yankunanmu, abin da za mu yi shi ne mu karfafa fasahar leken asirinmu don cafko marasa kishin kasa acikinmu sannan mu yi maganinsu ba tare da wani tausayi ba” in ji Zulum.
Ya yi kira da a sauya salon yaki da matsalar tsaro, yana mai yin Allah wadai da irin wannan kwangila da wasu ke amsowa don tada zaune tsaye.
A cewarsa, kawar da irin wadannan mutane, na iya maido da zaman lafiya cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp