‘Yan ta’adda sun farmaki wasu sojoji da ke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari da ke birnin tarayya Abuja.
Wasu rahotannin sirri sun bayyana cewar ‘yan ta’addan na shirin kai hari makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati a Abuja.
- Rashin Tsaro: Haramta Acaba ‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Za Su Rasa Aikin Yi – ACOMORAN
- Zamu Hukunta Duk Wanda Ba Musulmin Ba Da Ya Sake Keta Harami – Saudiyya
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin tarayya amma hukumomi sun ce suna kokarin gano maharan.
A cewar daya daga cikin majiyoyin, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi wa dakarun sojin da ke sintir a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna.
Ya kara da cewa sojoji uku daga cikin dakarun sun jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
“Harin da aka kai a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna nan a wurin kuma akwai yiwuwa su kai farmaki makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari kamar yadda aka ruwaito a baya,” inji majiyar.
Da aka tuntubi mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Birgediya-Janar, Godfrey Abakpa, ya tabbatar da harin, amma ya ce sun yi nasarar fatattakar su.
Ya kara da cewa an kwashe sojojin da suka jikkata zuwa asibiti kuma suna samun kulawa.
“An kai musu hari kuma an yi nasarar dakile harin. Muna da ‘yan tsiraru da suka samu raunuka amma an su kai asibiti domin ba su kulawa.
“A halin yanzu dakarunmu na bincike a yankin domin fatattakar ‘yan ta’addan da suka addabi yankin baki daya. Ana shawartar mazauna yankin su ci gaba da gudanar da sana’o’insu, su ci gaba da ba mu hadin kai ta hanyar ba mu bayanan da suka dace domin mu samu nasara gano wadanda suka kai hari,” inji shi.