Wasu ɓata-gari da ake kyautata zaton masu fafutukar kafa ƙasar Yarbawa ne, sun yi yunƙurin ƙwace babban ofishin Jihar Oyo da kuma ƙwace majalisar dokokin Jihar.
‘Yan ta’addan dai an ce sun rufe fuskokinsu ɗauke kuma da makamai a lokacin da suka isa sakatariyar jihar.
- Hanyoyin Da Za A Taimaka Wa Malamai Inganta Aikinsu (7)
- An Damke Wasu ‘Yan Nijeriya Kan Zargin Tilasta Wa Dan Australiya Tura Masu Hotuna
Wasu daga cikinsu kuma sun tare hanyar da ke zuwa gidan gwamnatin Oyo.
Wannan lamarin dai ya tayar da hankalin mazauna Agodi da ke birnin Ibadan, inda suka rika rufe shagunansu tare kuma da ƙaurwacewa unguwar da abun ke faruwa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba dai jami’an tsaro da ke jihar suka yi dirar mikiya, inda suka fatattake su bayan an yi musanyar wuta a tsakaninsu, wanda ya tilasta ‘yan ta’addan barin harabar sakatariyar da suka yi yunƙurin kwacewa domin ta zauna a ƙarkashin ikonsu.
Mai taimaka wa gwamnan jihar kan sha’anin tsaro, Sunday Odukoya (mai ritaya), ya ce ‘yan ta’addan sun so su saka tutarsu ne ta ƙasar Yarbawa a gidan Gwamnatin jihar na Oyo.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a bayyana cewa ko an kama wani daga cikinsu ba.
Bayan fatattakar da jami’an tsaro suka musu a lokacin da suka riske su, wanda ya tilasta su barin babban ofishin Jihar Oyo.