An kama mutum biyu a Nijeriya saboda zarginsu da yunkurin lalata da wani dalibi dan Australiya da ya halaka kansa.
‘Yansandan Australiya sun ce matashin da aka kashe ya yi musayar hotuna da wani mutum ta intanet kafin ya soma yin barazana da kuma neman kudi a hannunsa.
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
- Bikin Sallah: Ministan Yaɗa Labarai Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Dawo Da Kyawawan Dabi’un Da Suka Jingine
Bayan wani bincike da aka yi, an gano mutanen biyu da ake zargi a Nijeriya inda za su fuskanci shari’a.
‘Yansanda sun ce dabi’ar tilastawa mutum tura hotuna ta hanyar yin barazanar tona masa asiri musamman a tsakanin matasa na matukar karuwa.
Ba a fitar da bayanan yaron – shekarunsa da kuma inda yake zaune a New South Wales ba, an yi haka domin kare iyalinsa.
‘Yansanda a New South Wales sun ce wadanda ake zargin suna tilasta tura masu hotunan jikin mutum din matasa ne kuma sun ce sun yi barazanar tura hotunan matashin ga abokanai da kuma yan uwansa idan har ya ki biyansu Dala 330.
“Sakonnin sun yi muni. Sun matsa wa yaron lamba ya biya kudin,” in ji babban jami’in dansanda da ke yaki da laifukan intanet, Mathew Craft, kamar yadda ya shaida wa jaridar Sydney Morning Herald.
Yaron ya mutu ne ta hanyar kashe kansa a yammacin ranar da abin ya faru s shekarar da ta gabata.
‘Yansandan Australiya sun yi aiki tare da takwarorinsu a Afirka ta Kudu da Nijeriya wajen zakulo mutanen da ake zargi da aika-aikar a Nijeriya.
An gano shaidar da ke nuna matasan biyu sun yi kokarin karbar kudi a hannun mutane cikin wayoyinsu, a cewar jaridar ta SMH. An tuhume su da zargin tilasta wa yaron dan Australiya kwanciya da su amma ba mutuwarsa ba.