Daga Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Cikin bukukuwan cikar Nijeriya shekaru 57 da samun ‘yancin kai, Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya halarci bikin murnar zagayowar ranar wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Wannan shi ne karo na biyu da Gwamnan ya riska tun bayan samun nasarar zama Gwamna Kano a wannan shekarar da kuma shekarar da ta gabata. Idan za a tuna, ba a samu gudanar da irin wannan biki ba tun bayan wanda ya gudana a shekara ta 2012 sakamakon matsalar rashin tsaro da aka yi fama da ita a Arewacin ƙasar nan.
Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin taron, Gwamna Ganduje ya taya al’ummar Jihar Kano murnar zagayowar wannan rana mai daɗaɗɗen tarihi na samun ‘yancin kan ƙasa, saboda haka ya tabbatar wa jama’a da cewar haɗin kan ƙasar nan a matsayin ƙasa guda na nan daram kuma za a ci gaba a kansa, saboda haka ya buƙaci jama’a da su kauce wa duk wani abu da ka iya kawo rarrabuwar kan jama’ar Ƙasa.
Taron wanda ya samu halartar mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammmadu Sanusi II tare da wasu fitattun mutane irin su kakakin majalisar dokokin Jihar Kano, Alhaji Yusif Abdullahi Ata, sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji da sauran manyan jami’an gwamnatin Kano.