Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta samu nasarar kama mutum arba’in da biyar da ake zarginsu da laifin daba, sakamon kama su da muggan makamai a Kofar Na’isa da Kwanar Disu da ke karamar hukumar Gwale.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kanon, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Kabo.
Kamar yadda ya ce, “Ranar 26/06/2022 sun samu rahoton cewa, wasu gungun ‘yandaba dauke da muggan makamai sun rufe hanyar Kofar Na’isa da ta Kwanar Disu, da ke karamar hukumar Gwale a kokarinsu na kai wa mutannen wannan yanki farmaki donin yi musu sata”.
Ya ce, bayan da suka samu wannan labarin, nan da nan ‘yansandan suka bazama zuwa wannan guri inda suka samu nasarar kama ‘yandabar a “Filin Mahaha”.
Ya ci gaba da cewa, sun samu nasarar kama mutum arba’in da biyar wadanda kuma aka kama su da muggan makamai da kuma miyagun kwatoyi masu yawa.
Kiyawa ya ce, dukkan wadanda aka kaman sun tabbatar da cewa sun zo ne daga sassa daban-daban na unguwannin da ke Kano domin su tayar da hargitsi a wajen daurin aure kuma sun hadu a “Filin Mahaha” suka yi shaye-shayensu suka bugu.
Ya ce, kwamishinan ‘yansanda ya umarci a gudanar da bincike, sannan bayan gama binciken a mika wadanda aka Kaman zuwa kotu, domin su fuskanci hukuncin da ya dace.