Wani rahoto da majalissar gudanarwar kasar Sin ta mikawa majalisar wakilan jama’ar kasar a jiya Lahadi, ya nuna yadda yankunan arewacin kasar biyar, suka kunshi kaso 40 bisa dari na daukacin filayen noman kasar, inda suke taka muhimmiyar rawa wajen kare filayen noma.
An gabatar da rahoton ne ga zaman muhawara na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana a yanzu haka. Rahoton ya ce kaso 40 bisa dari na filayen noman kasar Sin da ya kai fadin kusan ma’aunin mu biliyan 1.93, kwatankwacin hekta miliyan 128.67, suna a yankunan arewacin kasar 5, da suka hada da lardunan Heilongjiang, da da Henan, da Jilin da jihohi masu cin gashin kai guda biyu wato Inner Mongolia da Xinjiang.
Har ila yau, a cewar rahoton, an samu karin fadin filayen noma a kasar, da mu miliyan 11.2, kwatankwacin hekta dubu 746.67, sama da wanda aka yi rajista yayin safiyon kasa karo na uku, sakamakon ci gaba da ake yi da kokari sannu a hankali, na fadada yawan filayen noma a yankunan kudancin kasar, da kuma tsare-tsaren doka masu nasaba da kare filayen noma. (Saminu Alhassan)