Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi ta ce zuwa yanzu ta fara bincike dangane da cire wa wani almajiri mai suna Najib Hussaini idonsa na hannun dama da wasu da ba an san ko su waye ba suka yi, a garin Kafin Madaki da ke cikin karamar hukumar Ganjuwa a jihar.
Yaron mai shekara 12 a duniya, ya zo almajiranci Jihar Bauchi ne daga Kano, inda ke koyon karatun Alkur’ani a Kafin Madaki.
- Kanu Ya Yi Tur Da Kai Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Kudu Maso Gabas
- Gwamnatocin Kananan Yankunan Sin Na Bayar Da Katunan Rangwamen Sayayya Domin Farfado Da Karsashin Kasuwanni
A sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, SP Ahmed Muhammad Wakil, ya fitar a ranar Talata, ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Disamnan 2022 a unguwar Yamma, unguwar da ba ta da nisa sosai da tsangayar su almajirin.
A cewarsa, wasu mutane biyu ne suka je inda yaron yake a kan babur kirar Bajaj, inda suka aike shi da ya taimaka ya shiga wani gida ya kira musu wata yarinya “Kwatsam suka dauke yaron a kan babur din suka wuce da shi wani kango kusa da Hayar Gonar Wakili, inda suka cire masa idon hannun dama ta karfin tsiya kana suka yasar da shi cikin jini a galabaice.”
Ya kara da cewa, a hakan yaron ya yi kokari ya rarrafa ya fita zuwa inda abokansa za su gan shi inda su kuma suka kwashe shi cikin hanzari zuwa wajen malamainsu.
Tunin aka kai rahoton faruwar lamarin ga caji ofis din ‘yansanda da ke Ganduja a lokacin da lamarin ya faru inda a nan kuma aka wuce da shi zuwa babban asibitin koyarwa na ATBUTH da ke Bauchi domin kokarin samar masa da agajin likitoci.
Wakil, ya kara da cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aminu Alhassan ya roki iyaye da a kowane lokaci suke kai rahoton duk wasu bata garin da basu yarda da su ba da suke yawo a kusa da unguwanninsu domin daukan matakan da suka dace na dakile aniyarsu ta aikata laifuka.
Ya bada tabbacin cewa wadanda suka aikata wannan danyen aikin za su shiga hannun hukuma ba da jimawa ba.