Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta cafke wani dan banga dan kasar Mali, Emmanuel Bori, mai shekaru 31 bisa zargin kashe Emmanuel Hamma Shehu da Almond Hamma Shehu kan rikicin gona.
An rawaito cewa wadanda aka kashe mazauna kauyen Bori ne da ke gundumar Koma a karamar hukumar Jada na jihar Adamawa.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce wanda ake zargin ya samu sabani ne da wadanda abun ya shafa kan wata gona da ke yankin Bori wanda ta yi sanadin haifar da rikici a tsakanin su.
Emmanuel ya yi amfani da bindigarsa wajen harbin wadanda abun ya rutsa da su, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp