Saura kwanaki biyu kacal ya rage a gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki, ‘yansanda a jihar Edo sun kama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Jarret Tenebe.Â
Rahotanni sun ce, an cafke Tenebe ne bisa umarnin mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu.
An rahoto kuma cewa, an kama Tenebe ne a mahaifarsa ta Ikabigbo da ke karamar hukumar Etsako ta gabas.
Sai dai, babu wasu bayanai kan dalilin kamun na sa.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APCn dai kasance cikakken dan siyasa ne kuma mai dimbin mabiya a cikin jam’iyyar APC a jihar.
Ya kuma kasance daya daga cikin masu yiwa tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole biyayya.
Tenebe a wani faifan bidiyo da aka fitar a kwanan baya, ya soki mataimakin gwamnan jihar akan wasu abubuwa na siyasa.
Shugaban APC na jihar kanal Divid Imuse mai murabus da kakakin APC a jihar Ofure Osehobo sun tabbatar da kamun da aka yiwa mataimakin.
Sai dai kakakin rundunar ‘yansanda na jihar , Chidi Nwabuzor bai fitar da wata sanarwar kan dalilin kamun ba.