Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu wajen kashe dan Sanata Kabiru Gaya, Sadiq Gaya.
Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja, DSP Josephine Adeh, ta ce mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan suna hannun ‘yansanda yayin da ake ci gaba da bincike.
Sai dai rundunar ‘yansandan ba ta bayyana sunayen wadanda ake zargin da ake tsare da su ba domin kada ta yi kasa a gwiwa wajen gudanar da bincike.
A cewarta, “An kama mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan kuma ana ci gaba da bincike. Za a sanar da sakamakon binciken daga baya.”
An kashe dan Sanatan daga Jihar Kano ta Kudu, wanda ke aiki da hukumar kula da kadarorin Nijeriya (AMCON), a ranar Talata a Abuja.
Mahaifin marigayin, Sanata Kabiru Gaya, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa a hukumar zabe mai zaman kanta, kuma tsohon gwamnan Jihar Kano ne kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu.