‘Yansanda sun yi ruwan barkonon tsohowa ga wadanda suka shiga gangamin nuna goyon baya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi a ranar Asabar.
Wadanda suka shirya da magoya bayansu da suka hadu a layin Mile 50 domin gudanar da gangamin goyon bayan Obi an tsaida su kana aka hana su wucewa zuwa kan layuka.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutane 5 Da Ake Zargi Da Hannu A Kisan Dan Sanata Gaya
- Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Usman Bala
Daya daga cikin masu gangamin, Nwali Ikechukwu ya shaida wa majiyarmu cewa, an jikkata wasu daga cikinsu.
Har zuwa lokacin hada rahoton ba a samu ji ta bakin kakakin hukumar ‘yansanda na jihar Ebony, SP Chris Anyanwu ba.
A wani labari makamancin wannan, magoya bayan Peter Obi da abokin takararsa Datti Baba Ahmed, sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya a Umuahia, babbar birnin jihar Abia a ranar Asabar.
Hukumar zabe mai zaman kanta dai ta ware ranar 28 ga watan Satumba a matsayin ranar fara gangamin yakin neman zaben 2023.