Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da laifukan hada baki da yin barazana ga rayuwa da cin zarafi da kuma yunkurin yin garkuwa da mutane.
Kakakin Rundunar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Bauchi.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Bayan Garkuwa Da Shi A Jihar Bauchi
- ‘Yansanda Sun Hallaka Ɗan Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutun 6 A Bauchi
Ya ce rundunar da ke yaki da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka, na ci gaba da samun sakamako mai kyau.
“A ranar 7 ga Maris 2024 da misalin karfe 1400, wani mai suna Yahaya Adamu, daga kauyen Badakoshi karamar hukumar Bauchi, ya kai kara ga sashin yaki da masu garkuwa da mutane (AKU) da ke sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
A cewarsa, wanda ya shigar da karar ya ce a ranar 4 ga watan Maris, da misalin karfe 2030, wani da bai san sunansa ba ya kira shi ta waya ya gabatar da kansa gare shi.
“Ya yi masa barazanar cewa zai samar da Naira miliyan 5.”
A cewar ’yan sanda, wanda ya kira wayar ya yi barazanar tattara ’yan kungiyarsa don yin garkuwa da shi (Yahaya), ko kuma danginsa.
Bayan kwanaki kadan, wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane sun aika masa da bayanan asusunsu, ta hanyar amfani da asusun kasuwanci na (POS) don saka kudin da suka nema, cewar Wakil.