Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wani Abubakar Abdulaziz mai shekaru 30 da haihuwa da laifin yin garkuwa da wani yaro dan shekara uku da haihuwa a karamar hukumar Musawa ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Gambo Isah, ya fitar ranar Litinin a Katsina.
- INEC Ta Dakatar Da Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa
- Karamar Sallah: Gwamnatin Borno Ta Biya Ma’aikata Albashin Afrilu
“A ranar 23 ga watan Maris, da misalin karfe 01:00 na dare, wanda ake zargin ya shiga gidan Adamu Alhassan da ke kauyen Bacirawa, karamar hukumar Musawa, ta Jihar Katsina da laifin aikata laifi, a lokacin da yake barci mai nauyi ya yi garkuwa da dansa mai shekaru uku.
“Ya ajiye masa takarda, inda ya umarci Alhassan da ya biya kudin fansa N800,000 kuma ya ajiye lambar za a neme shi,” inji shi.
Isah ya ce mahaifin ya tuntube shi, ya tattauna kuma ya biya Naira 150,000 domin a sako yaronsa, “amma abin ya ci tura”.
Kakakin ya ce bayan samun rahoton mahaifin, jami’an hukumar sun zage damtse, inda suka zakulo wanda ake zargin tare da kama shi.
“A yayin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin kuma ya kara da cewa ya birne yaron da ransa bayan ya karbi kudin fansa,” in ji shi.
Isah ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.