Rundunar ‘Yansandan jihar Kebbi ta cafke wasu mutum uku da ake zargin su da yin jabun kudi da ya sama da naira miliyan goma sha bakwai (N17,000,000) a garin Warra da ke karamar hukumar Ngaski.
An gano kudaden jabun tare da taimakon kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) a tashar mota ta Warra.
- Hukumar Kwastam Ta Kama Haramtattun Kaya Da Kudinsu Ya Kai Naira Miliyan 91.5 A Kebbi
- Za Mu Tabbatar Da Nasarar Tsarin Ba Da Inshorar Kiwon Lafiya A Kebbi – Dakta Augie
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ahmed Magaji Kontagora, ya ce wadanda ake zargin ‘yan asalin kauyukan Gungun Tawaye ne da Chupamini, a karamar hukumar Ngaski, yayin da ake ci gaba da bincike, nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.
Kwamishinan ya kuma jaddada cewa, wadanda ake zargin sun hada da Faruku Zubairu Musa da Salisu Mohammed dukkansu maza daga Karamar hukumar Ngaski ta jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp