Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke shirin kai hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Yola.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Litinin a Yola.
- Ministar Ghana Ta Yi Murabus Bayan Sace Makudaden Kudade A Gidanta
- Kotu Ta Kori Dan Majalisar LP, Omolie, Ta Ayyana Elumelu A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe
Ya ce jami’an tsaron da ke gidan Abubakar ne, suka kama daya daga cikin wadanda ake zargin, yayin da daya kuma aka kama shi a wani wuri a babban birnin jihar.
“Daya daga cikin wadanda ake zargin, mai shekara 29, ya amsa cewa shi dan Boko Haram ne daga Damboa a Jihar Borno.
“An kama shi ne a kofar gidan Atiku Abubakar a lokacin da yake kokarin kai hari da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi.
“Sun ce an aiko su ne domin su yi shawagin gidan da wasu wuraren da za su kai hari,” in ji shi.
Nguroje ya ce an mika wadanda ake zargin ga hukumomin sojin domin ci gaba da bincike tare da daukar mataki.