‘Yan sanda a jihar Gombe sun cafke ‘yan daba guda 23 masu yin ta’addanci cikin dare a jihar Gombe.
‘yan daban wadanda aka fi sani da ‘Yan kalare sukan tare al’umma da larura ta fito dasu wajen Gidajen su da dare suyi musu kwace a garin na Gombe.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya kira a hedikwatar ‘yan sandan yayin baje kolin wadanda aka cafke daga cikin masu Laifin.
A cewar sa, sashin rundunar ‘yan sanda na musamman mai taken ‘999’ wanda aka kafa don yaki da ‘Yan kalaren ne suka samu nasarar cafke masu laifin bayan samun rahoton sirri inda maboyarsu take a unguwar Malan-Inna dake cikin garin Gombe.
“Bayan an kama su, yan sanda sun kwace makamai da suke amfani da su wajen aikin ta’addancin da suka hada da adduna guda goma sha biyar da sauran wasu makamai.
“Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu. Za mu gurfanar da su a gaban kotu da zarar mun kammala Bincike” Inji kakakin rundunar ‘yan sandan, Mahid.