Rundunar ‘yansandan Jihar Legas ta cafke wata mata mai shekara 53 dauke da kayan aikin zabe a jihar.
Matar wadda har yanzu ba a bayyana sunanta ba, ta shiga hannun hukuma ne a wata cibiyar kasuwanci da ke Baruwa, Iyana Ipaja da ke Legas yayin da take kwafin kayan zaben da ake zargin na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ne.
- A Wata Daya ‘Yansanda Sun Gano Bindiga 182 Da Harsasai 430
- A Wata Daya ‘Yansanda Sun Gano Bindiga 182 Da Harsasai 430
An cafke ta ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis a kan titin Candos da ke yankin Baruwa, kamar yadda kakakin ‘yansandan jihar, Benjamin Hundeyin ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar.
Ya ce, an kama matar ne a cikin wata cibiyar kasuwanci yayin da take kwafan takardun zabe da yawansu ya kai 550 kala daban-daban.
Kakakin hukumar ya ce matar ta kasa ba su cikakken bayanin yadda ta samu kayan zaben da kuma dalilin da ya sanya take rubanyasu ko me za ta yi da sh.
“Mun cafke ta kwamfuta da ta ke amfani da ta wajen sarrafa kayan, kuma ba ta bada cikakken bayanin yadda ta samu kayan ko abun da za ta yi da su ba.”
“An tura ta zuwa sashen Binciken manyan laifuka CID Yaba domin fadada bincike.”