Rundunar ’yansandan Nijeriya tare da haɗin guiwar ‘yansandan ƙasa da ƙasa (INTERPOL) da ke Abuja, ta ceto wani mutum ɗan asalin ƙasar Ghana mai suna Sammed Iddrisu, wanda aka yaudare shi zuwa Nijeriya da sunan taimaka masa don ya samu takardun tafiya Turai.
An ceto shi a ranar 27 ga watan Yuni, 2025, a Abuja bayan samun sahihan bayanai daga ofishin INTERPOL da ke Accra, Ghana, a ranar 16 ga watan Yuni, 2025.
- Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi
- Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang
Kakakin rundunar ’yansanda na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce binciken farko ya nuna cewa a ranar 10 ga watan Janairu, 2025, mahaifin Sammed, Mista Nartey Louda, ya biya wani mutum mai suna Attah kuɗi har GHC 55,000, wanda ya yi masa ƙarya cewa zai taimaka wa ɗansa wajen samun biza zuwa Faransa.
Sammed ya amince inda aka ce ya tafi Abuja domin karɓar takardun.
Amma da ya isa Abuja a ranar 25 ga watan Yuni, 2025, sai aka tsare shi ba bisa ƙa’ida ba, aka tilasta masa shiga wata harkar damfara ta yanar gizo da ke da alaƙa da kamfanin QNET – wata harkar kasuwanci da ke ɓoye a matsayin kamfanin hada-hadar kasuwanci a Intanet.
Wani ɗan Ghana da aka yi ƙoƙarin yaudararsa shi ma ya tsere, ya koma Ghana, inda ya kai rahoto ga hukumomi, abin da ya haifar da haɗin gwiwar ƙasashen biyu don ceton Sammed.
Sakamakonhaɗin gwiwar da ’yansanda suka yi a Abuja, an ceto Sammed.
Adejobi ya ce an ɗauki matakai don kama waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki domin su fuskanci hukunci.
A wani samame daban, ’yansanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma ta’addanci a Abuja da Jihar Kaduna.
An kama su ne a ranar 29 ga watan Yuni, 2025, bayan samun sahihin bayani da kuma haɗin kai ƙarƙashin jagorancin ACP Victor Godfrey.
An kama su a wurare daban-daban ciki har da Mpape da Wukushi a Abuja da kuma Rijana a Jihar Kaduna.
Kakakin rundunar ’yansandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce waɗanda aka kama suna daga cikin gungun masu laifi da ke da sansanoni a dazukan Kachia da Rijana, inda suke tsare waɗanda suka sace na tsawon lokaci.
Hakazalika, an danganta su da wasu hare-hare da suka faru a Jere, Kajuru da wasu sassan Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp