ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Haɗarin Da Ke Ƙunshe Da Jin Ɓangare Ɗaya Na Labari

by Azu Ishiekwene, Sani Anwar and Muhammad
11 months ago
Da

Akwai wani ɓangare na aikina da zai iya haxiye baki-ɗaya. An tarbiyantar da ‘yan jarida, wajen neman abincin da manyan kayan haxinsa sun ƙunshi aikata laifuka da gangan, abin da ya shafi tsakanin namiji da mace da kuma kuɗi. Komai kuwa bayan wannan, ajiye shi a gefe ake yi. Shi yasa, idan ka bibiyi abubuwan da ake karantawa a jaridu, rediyo, talabijin ko kuma abubuwan da ake yaxawa a kafafen yaxa labarai na intanet, wani lokaci sai ka yi tunanin cewa; kamar ana daf da fara tura duniya wilbaro.

Daga rahotannin masu tayar da hankali na kashe-kashen Jihohin Benuwai da Filato zuwa labaran sace-sacen mutane don neman kuxin fansa, sauran ayyukan ta’addanci da qananan laifuka; ba a samu sauƙi daga waɗannan munanan labaru ba. Haka zalika, tun daga yakin Ukraine har zuwa varnar da aka yi a Gabas ta Tsakiya da Tekun Fasha, labaran babu daɗin ji.

  • Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato

Labari mara kyau yana da daxin ji?

ADVERTISEMENT

Ba don ɗabi’ar yawaitar munanan labarai daga ‘yan siyasa da sauran abokan hulɗoɗinsu ba, da rahotannin da ‘yan jarida ke fitarwa ba zai taɓa zama mummuna ko maras daɗi ba.

Rikici ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya, PDP, jam’iyyar LP, ita ma ta shiga ruxani. Jam’iyyar SDP, cikin tsaka mai wuya. Haka nan, wani juyin mulki ya hamvarar da shugaban jam’iyyar APC mai mulki da rana tsaka, sannan kuma ana shirin kafa jam’iyyar haxin gwiwa da ke fuskanta haɗa ƙwanji da jam’iyya mai mulki.

LABARAI MASU NASABA

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

A ɗaya ɓangaren kuma

Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; waxanda labarai a kansu babu daxin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, waxanda galibi labaransu marasa daxi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; waxannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma haxari duk da ke xauke cikin wannan labari.

Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna fuskantar qalubale na yi wa al’umma aiki ta hanyar samar da damammaki, rage talauci da kuma tsantseni wajen sarrafa dukiyar al’umma.

Duk da cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba, amma abin da na gani a xan wannan lokaci da na ziyarci waxannan jihohi uku, tattakina zuwa Jihar Zamfara; shi ne mafi matuqar tsoro a wajena

Zuwa Gusau

A karon farko da aka gayyace ni zuwa babban birnin jihar, Gusau, sai na yi watsi da tafiyar. Domin kuwa, a tafiya irin wannan akwai buqatar yin tunani da nazari mai zurfin gaske, musamman ganin yadda nake samun munanan labarai a kan Ado Aliero da sauran tawagarsa ta ‘yan ta’adda da ke yankin.

Har ila yau, sai aka sake turo min da wata gayyatar. Amma dai, a wannan karon akwai ɗan qwarin gwiwa, musamman ganin cikin tawagar da zan bi na tattaunawa ta farko da za a yi da Gwamna Dauda Lawal kai tsaye a kan wa’adin shekaru biyu da ya kwashe kan mulki. Tawagar ta qunshi; Gbenga Aruleba daga gidan talajin na AIT, Reuben Abati, ARISE TV da matarsa, Kiki, sai Ahmed Shekarau daga Media TRUST, Onuoha Ukeh daga SUN da kuma Babajide Otitoju, wanda Olajumoke Olatunji ya maye gurbinsa daga TVC.

ChatGPT da Gusau

Amma fa akwai matsala. Ta yaya za mu isa Gasau, duk da sanin abin da muka sani, na tambayi ‘ChatGPT’. Sai amsa min da cewa, kada ku tafi idan har tafiyar ba mai muhimmanci ba ce.

Ya ba da sanarwar tafiye-tafiye daga ofishin harkokin waje na burtaniya, Australia, Canada da kuma Amurka tare da gargaxi game da tafiye-tafiye saboda tashin hankali, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yana mai bayyana cewa; “Babbar matsaya daga hukumomin kula da tafiye-tafiye, ba ta ba da shawarar yin tattaki zuwa Jihar Zamfara, idan har ba akwai buqatar yin hakan ba.

“Titin Zariya zuwa Zamfara, musamman Funtua da ke Jihar Katsina, Tsafe, Maru-Dansadau, an bayyana su a matsayin wasu yankuna na mutuwa, wato wani filin wasa ne na Dogo Gide da Bello Turji, wanda tawagarsu ta ‘yan ta’adda suka kashe matafiya aqalla 20, kamar yadda rahoton AP ya bayyana a watan Afrilun wannan shekara. Ina kan hanya, amma na qudiri niyyar tafiya.

Mutuwa da dawowa

Na yi ta mutuwa ina dawowa a cikin awa biyu da minti sha biyar, tsoro ya gama kama ni tare da alhinin cewa; idan na mutu a shekara 60, ba wai na mutu da ƙuruciya ba ne. Ban san cewa, matata ta lallava ta sanya min wani abin kariya a cikin wata ‘yar ƙaramar kwalba.

Gaba-xaya ban lura ba, sai da na dawo daga tafiyar ina goge jakata, wannan ya isa ta bugi qirji da cewa; ta taimaka min da wani sirri na kariya. Na kasance a ankare cikin tsawon wannan tafiya ta kimanin kilomita 450 daga Abuja, cike da ximuwa.

Abin da ya ba ni mamaki, titin da ke tsakanin Zaiya da Katsina, mai layi biyu ne, sannan kuma yana da kyau sosai; titin bai tsuke ba sai da muka shiga Katsina, kana kuma ya sake buɗe bayan mun yi nisa ga duwatsu masu ban sha’awa da tsaunika da dukkanin vangarorin titin biyu. Amma titin Abuja zuwa Kaduna, abin kunya ne idan aka kwatanta shi da wannan, amma duk da haka; babban titin Abuja zuwa Kadunan ya lalace, kai ka ce shi ne qofar shiga Arewa Maso Yamma.

Fargaba da ɗimuwa…

Bayan Zariya, a wasu lokuta, mun wuce garuruwa masu yawan jama’a, amma mafi shahara a cikinsu shi ne garin Funtua, garin wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da suka haxa da marigayi Malam Ismail Funtua da kuma fitaccen xan kasuwa, Umaru Mutallab.

Kowa ya yi tsit, kuma na kasa tambayar kaina cewa; ko mutanen da ke zaune a qauyukan da qananan garuwan da muke ratsawa, sun san abin da ake faxa game da su kafafen yaxa labarai? Yayin da muka shiga Tsafe, garin xaya daga cikin manyan ‘yan ta’addan da suka yi qaurin suna wajen garkuwa da mutane, waɗanda suka samu nasarar share wajen zama a Jihar Katsina kafin ziyarar tamu, duk gashin da ke jikina sai da ya tashi.

Duk da cewa, mun samu rakiyar jami’an ‘yansanda ga kuma shingayen sojoji da dama a hanyar, yayin da muka isa Tsafe, kilomita 48 zuwa Gusau, ba ku ga irin tsoro da firgicin da ke cikin motarmu ba. shiru kake ji kowa ya yi xif.

Bayan Tsafe, na yi zaton tashin hankali ya qare a wannan tafiya. Sai kuma na ji na samu sauqi tare kuma da shiga ruɗani da muka shiga Gusau. Sauqin shi ne da muka isa lafiya, ruxanin kuma saboda titi mai hannu biyu da ake dab da kammala, wanda ya haxe da na Zamfara mai tattare da haɗari da ban tsoro a tare da shi.

An samu canji

Ashe da rabon zan ga irin waxannan al’amuran a Enugu, inda rabo da zuwa tun
2006 (lokacin Chimaroke Nnamani yana gwamna). Ziyarar da na yi zuwa Zamfara na yi ta tun a farkon shekarun 1990, lokacin tana haɗe da Jihar Sakkwato. Bayan wani Kantoman Mulkin Soji xaya, da kuma wasu gwamnonin farar hula huxu, kafin Dauda, na biyar, Zamfara ta kasance wani abu kamar tallan shirin wasan kwaikwayo na Kannywood, inda ‘yan siyasa ke kwashe dukiyar qasa, ciki har da jama’arta, tare da nuna iko

ko shakka babu Dauda zai iya nuna bambanci a wannan tsari. A cikin shekaru biyu, ya inganta asibitocin tuntuva da ke Gusau zuwa asibitin koyarwa mai xauke da wasu kayan aiki na zamani, ya kuma inganta harkar samar da ruwan sha, sannan ya kawar da koma bayan kudin WAEC da NECO na dalibai, lamarin da ya sa jihar ta kasance da ta samu kyakkyawan sakamako na tsawon shekaru. Haka kuma ya gina sabon filin jirgin sama wanda za a iya budewa kafin Satumba.

Gwamnati ta ce ta biya basussukan gratuti da kuma fansho ga ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha tun daga shekarar 2011, da aka kiyasta kudin sun kai Naira biliyan 13.6, baya ga biyan bashin albashin watanni hudu da ya gada tare da kara mafi karancin albashi daga Naira 7,000 duk wata zuwa Naira 70,000.

“Komawar harkoki”

A lokacin da ake tattaunawar kai tsaye da Abati ya tambayi Dauda yadda ya sanya jihar a kan turba mai ban sha’awa, ciki har da ba ta wutar lantarki ta farko tun bayan da aka kirkiro ta shekaru 29 da suka gabata, gwamnan ya ce hakan ya faru ne ta hanyar toshe leken asiri ta hanyar amfani da fasaha, da kuma ba da fifiko wajen bunkasa albarkatun jama’a da kuma inganta karfinsu.

Ya ce an kuma yi amfani da fasaha don tattarawa da yin amfani da bayanan sirri don gina jiha mafi aminci, yana mai shan alwashin cewa ba za ai yi sulhu da ‘yan fashi da masu laifi ba.

Idan rayuwar dare ta daidaita a Gusau, babu shakka dukkan jama’ar da suka rasa matsugunai da wuraren sana’a za su dawo inda suke musamman gonaki a hankali. Wannan kuma wani hangen nesa ne da mutum zai iya duba jihar da aka ayyana kusan shekaru talatin ta hanyar cusa tsattsauran ra’ayi na addini, sata da kuma ‘yan fashi.

Ishiekwene Babban Editan LEADERSHIP kuma mai Rubuce-rubuce a Kafofin watsa labarai da harkokin Kudi.

Da
Azu Ishiekwene
+ posts Bio
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Su Wa Ke Fatattakar Obi Da Kwankwaso?
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
Da
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Sojoji Sun Ceto Mutum 92 Tare Da Daƙile Harin Ƴan Ta’adda A Borno
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Uzodimma: Babu Dimokraɗiyya Idan Babu Hamayya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Alamomin Fara Ruɓewar Hannu Bayan Ɗorin Gida
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ministocin Da Suka Ajiye Muƙamansu Ba Su Samu Tikitin Takara Ba
Da
Muhammad
+ posts Bio
  • Muhammad
    Cikin Shekaru 28, Kudiri Ƙasa Da 10 Sanatocin Zamfara Ta Arewa Suka Gabatar A Majalisa – Shinkafi
  • Muhammad
    2027: NNPP Ta Yi Wa Korarrun Mambobinta Afuwa, Ta Yi Alƙawarin Basu Tikitin Kai-tsaye
  • Muhammad
    Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
  • Muhammad
    Kwankwaso Tamkar Tsuntsu Ne A Siyasa Da Yake Sauya Sheƙa Daga Nan Zuwa Can – Ganduje

MASU ALAKA

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
Labarai

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
‘Yansanda Sun Kama Barayi 15, Sun Kwato Motocin Sata 20 A Kano

’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.