Rundunar ‘yansanda Jihar Legas ta ceto wani yaro mai suna Emmanuel Adeleke daga hannun wanda ya sace shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a shafinsa na Twitter da kamfanin dillancin labarai (NAN) ya sanyawa hannu.
- Dakarun Soji A Jihar Kaduna Sun Kara Kashe Wani Jagoran ‘Yan Bindiga Gudau Kachalla
- Ganduje Ya Karrama Dan Sandan Da Ya Ki Karbar Cin Hancin Dala $200,000 A Kano
Ya ce yaron mai shekaru tsakanin 11zuwa 14, ya kubuta, don haka aka kai shi asibiti inda yake jinya a can.
“Abin da zamu iya cewa, an sace shi ne a Jakande, unguwar Ikotun a Legas a ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamba, 2022. Ya ba da sunansa a matsayin Emmanuel Timilehin Adeleke.
“Ya ba da sunayen iyayensa da adireshi daban-daban. Yana da shekaru tsakanin 11 zuwa 14.”
Hundeyin ya bukaci duk jama’a da su bayar da bayanai da za su taimaka inda za a gano iyayen yaron suke.
“Duk wani bayani da zai taimaka wajen gano iyayensa ko masu kula da shi zai taimaka,” in ji kakakin rundunar.