Akalla mutane shida da ake zargi da hannu a kisan da ya haifar da tarzoma a kasuwar Gosa da ke kan titin filin jirgin sama a Abuja, jami’an rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya suka kama.
Lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin ‘yan kasuwa da mazauna yankin, ya biyo bayan mutuwar wani mutum da ake zargi da satar dawa.
- Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
- 2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi
Sakamakon lamarin, da dama sun daina zuwa kasuwar, inda ake kallon ta a matsayin daya daga cikin mafi araha wajen sayan kayan abinci a Abuja.
Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a Abuja, Kwamishinan ‘yansandan, Adewale Ajao, ya ce biyo bayan faruwar lamarin, ‘yansandan sun yi gaggawar shiga yankin domin kwantar da hankula tare da dawo da zaman lafiya.
Ya ce, “An tuhumi wani matashi da laifin satar wani buhun dawa a kasuwa, sai wani mutum ya yanke shawarar daukar doka a hannunsa, abin da ya jawo rikicin.
“Bayan ’yansanda sun yi gaggawar shiga yankin domin kwantar da hankulan jama’a tare da dawo da zaman lafiya, a halin yanzu akwai mutane shida da ake zargi suna tsare a kan lamarin.”
Ya kara da cewa, ‘yansandan sun hada kan shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya wajen tattaunawa, wanda hakan ya taimaka wajen kwantar da hankula.
“Bayan faruwar lamarin, sai muka gana da shugaban al’umma a wurin, sarkin gargajiya yana tare da mu, muka tattauna kuma muka yi kokarin gano abin da ya faru, suka tabbatar mana da cewa za a wanzar da zaman lafiya,” in ji shi.
Ya ce har zuwa ranar Alhamis, Kasuwar Gosa ta koma ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tsauraran matakan sa ido kan ‘yan sanda.
Ajao ya kara da cewa, a kokarin da ake na magance matsalar fashi da makami, wasu laifuka biyar na fashi da makami sun kai ga kama wasu mutane 17, yayin da aka kama wasu 6 da ake zargi da hannu a fashin da aka dakile a Apo da Kubwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp