’Yansanda sun gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zuwa Abuja domin amsa tambayoyi kan rikicin da ya faru yayin hawan sallah, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami’in sa-kai, Surajo Rabiu, tare da jikkata wani mutum ɗaya.
Rikicin ya faru ne a ranar Sallah lokacin da tawagar Sarkin ke dawowa daga filin Idi zuwa fada, duk da haramta hawan da ’yansanda suka yi saboda dalilan tsaro.
- Kofin Duniya: Kocin Nijeriya Na Fatan Matashin Ɗan Wasan Arsenal Nwaneri Ya Wakilci Ƙasar
- Wutar Lantarki: Badaƙala Da Cin Zalin ‘Yan Nijeriya
A cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan wata 4 ga watan Afrilu, 2025, wadda CP Olajide Rufus Ibitoye ya sanya wa hannu, rundunar ta bayyana gayyatar Sarkin.
“Bisa umarnin Sufeton-Janar na ’Yansanda, ta hannun Mataimakin Sufeto-Janar na Sashen Bincike (FID), na ba ni damar gayyatarka zuwa bincike kan abin da ya faru a lokacin bukukuwan Sallah a jiharka.”
An buƙaci Sarkin da ya bayyana a hedikwatar Sashen Bincike na Musamman (FID) da ke Abuja, da misalin ƙarfe 10 na safe ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025.
Wani jami’in ’yan sanda ya shaida wa Leadership cewa: “Duk da haramta bukukuwan sallah, an gudanar da hawa a motocin Sarkin a rana ta uku bayan Sallah, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani bayani daga fadar Sarkin Kano game da gayyatar da aka yi masa.
Ga hoton takardar gayyatar da ‘yansandan suka fitar:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp