Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara ta kashe ‘yan bindiga uku tare da kwato bindiga kirar AK-49 da kuma bindigar famfo a wani samame da ta kai wa ‘yan bindigar a cikin kananan hukumomi Tsafe da Bakura.
Sabon kwamishinan ‘yansandan Jihar, Muhammed Bunu ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar a ranar Laraba.
Kwamishinan ya dauki alkawarin yakar masu aikata miyagun laifuka, “Kuma wannan shi ne kudirin babban Sufeto-Janar na ‘yansandan Nijeriya, Usman Alkali Baba na ganin an kare rayukan al’umma a fadin kasar nan baki daya.”
Bunu ya kuma yaba wa ‘yan jarida bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayar wa wajen ganin an kawo karshen masu aikata laifuka da suka addabi Jihar Zamfara.
Kwamishinan ya bayyana cewa, ‘yan fashi da makami, hare-haren ramuwar gayya, sace-sace da garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da kuma bangar siyasa a matsayin kalubalen tsaro da ke addabar jihar ta Zamfara, kuma sai yi kokarin kawo karshensu.
Rundudar ‘yansandan da ke karkashin sa za su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda ya dace da da’a, “Ba za mu amince da cin zarafin dan adam, cin hanci da rashawa da sauran ayyukan da suka saba wa doka ba.”
Kwamishinan ya yi kira da a ci gaba da ba da goyon baya, hadin kai, da hadin gwiwa daga kowa da kowa ta hanyar ba da bayanai masu amfani a kowane lokaci ga ‘yan sanda ga masu aikata laifuka domin daukar matakin gaggawa.