Rundunar ‘yansandan Jihar Neja ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Gurara a jihar a ranar Juma’a.
Rundunar a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP W. A. Abiodun, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, ta ce tun a ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 10:30 na safe, bisa ga bayanan da aka samu cewa an ga wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne.
- Son Rai Da Rashin Cancantar Jarumai Ke Gurbata Al’adu A Fina-finanmu –Daushe
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)
DPO na reshen Lambata da ke karamar hukumar Gurara, ya tara tawagar ‘yansanda tare da ’yan banga zuwa yankin, inda suka cafke mutane biyun da ake zargin.
“Lokacin da ake yi musu tambayoyi, sun amsa cewa suna cikin kungiyar masu garkuwa da mutane suka addabi yankin Gwagwalada a Abuja, Lambata da Kafin-Koro.
“An kwato wayoyin hannu guda uku daga hannun wadanda ake zargin, sannan kuma an samu kudi miliyan biyu da na5ira dubu dari da suka karba a matsayin kudin fansa domin a sako mutanen biyu da suka sace a Gwagwalada.
“Sun kuma kara da cewa sun ajiye wadanda suka yi garkuwa da su a dajin Gwalo.
“An ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun samu rauni ba, an kai su cibiyar lafiya ta FCM domin kula da lafiyarsu, sannan an mika su ga iyalansu,” in ji kakakin.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ogundele J. Ayodeji, ya tabbatar wa jama’a cewar rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta don tabbatar da tsaro a jihar.