Rundunar ‘Yansandan Jihar Kaduna, ta kama wani kasurgumin dan bindiga, wanda ya yi kaurin suna wajen satar mutane a jihar.
Wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar, ASP Mansir Hassan ya fitar, ta bayyana cewa, an kama Saidu ne a ranar 22 ga watan Maris, 2024.
- Ya Kamata Amurka Ta Yiwa Duniya Bayani Game Da Matsalolin Da Jiragen Kamfanin Boeing Ke Fuskanta
- Takaicin Fyaden Kananan Yara Ya Sa Na Shirya Fim Din AKASI – Yakubu Gwammaja
Ya kara da cewa wanda ake zargin ya kuma amsa laifin kai munanan hare-hare a jihar.
Idan za a tuna, a ranar 7 ga watan Satumba, 2023, ne mahara suka kai hari cocin Katolika ta St. Raphael, da ke yankin Kamantan, inda suka sace mutane ana tsaka da ibada.
Yayin harin, ‘yan bindigar sun kone gidaje da dama da dukiya mai tarin yawa a yankin.
Kazalika, a lokacin harin sun kashe wani dalibi sannan suka raunata mutane da dama, kafin daga bisani suka yi awon gaba da wasu a yankin.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ali Audu Dabigi ya yaba wa rundunar kan yadda suke ci gaba da kai wa jama’ar jihar dauki.
Amma ya bukaci jama’ar jihar, da suke bai wa jami’an tsaro hadin kai domin su ci gaba da yakar masu aikata laifuka a fadin jihar.