Rundunar ’Yansandan Jihar Jigawa ta kama mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da wasu mutane 156 bisa laifuka daban-daban cikin watanni biyu da suka gabata.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, CP Dahiru Muhammad ne, ya shaida wa manema labarai cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Adamu Musa mai shekara 47 daga unguwar Yalwawa a Dutse, shugaban masu garkuwa da mutane ne.
- Ci Gaban Sojojin Sin Yana Hidimar Manufar Zaman Lafiya A Ko Da Yaushe
- Sojoji Sun Kama Ɗan Bindiga Ɗauke Da Makamai A Jihar Filato
Ana zargin ya yi garkuwa da mutane huɗu daga ƙaramar hukumar Sumaila ta Jihar Kano, inda ya tsare su a ƙauyen Baranda na ƙaramar hukumar Dutse.
Ya saki mutanen ne bayan ya karɓi kuɗin fansa har Naira miliyan takwas da babur ɗaya wanda darajarsa ta kai Naira miliyan ɗaya.
Haka kuma, a ranar 29 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 3 na rana, ’yansanda tare da jami’an sa-kai sun kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane da fashi makami ne.
Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano.
Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi.
An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa.
Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mutane huɗun da ake zargi da hannu a garkuwar da ta faru a Sumaila, da ke Jihar Kano.
A wani lamari kuma, ’yansanda sun kama mutane huɗu da ake zargi da fasa shago a ƙaramar hukumar Malam Madori.
Waɗanda aka kama sun haɗa da: Nuhu Yusif Saleh (19), Hassan Ibrahim (19), da Nura Musa (22).
An ƙwato akwati mai ɗauke da kuɗi Naira 870,000, abun cajin waya guda biyu, na’urar PoS, wayoyi guda 20, da lasifiƙa daga hannunsu.
Jimillar mutanen da aka kama a cikin watanni biyu sun kai 156 bisa laifuka daban-daban, ciki har da safarar makamai, fashi da makami, kisan kai, fyaɗe, lalata kayan gwamnati, fataucin miyagun ƙwayoyi da sata.
Kayan da aka ƙwato sun haɗa da bindiga AK-47 guda biyu, motoci guda uku, adaidaita sahu guda ɗaya, wayoyi guda 23, shanun sata guda 14, da kuma miyagun ƙwayoyi kamar tramadol, diazepam, exol, tabar wiwi, da sauransu.
CP Muhammad ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da laifuka da kuma safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin Jihar Jigawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp