’Yansanda a Jihar Katsina sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar makamai tare da ƙwato bindiga da harsasai.
Mai magana da yawun ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, ya ce an kama mutanen biyu; Abdussalam Muhammed (mai shekaru 25) da Aminu Mamman (mai shekaru 23) da safiyar ranar Litinin, da misalin ƙarfe 4:35 na sace a kan titin Ingawa zuwa Karkarku, a mota ƙirar Volkswagen Golf.
Binciken cikin motar ya gano bindiga ƙirar GPMG ɗaya da harsasai sama da 1,200 da aka ɓoye a ciki.
’Yansanda sun ce an yi safarar makaman ne daga Jihar Jigawa zuwa Katsina domin bai wa ’yan ta’adda.
A yanzu haka, mutanen biyun suna hannun ’yansanda yayin da ake ci gaba da bincike.
Sufeto Janar na ’Yansanda, Kayode Egbetokun, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani domin taimaka wa yaƙi da laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp