Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane guda biyu da suka kware wajen yi wa ‘yan bindiga safarar makamai a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Mista Mansir Hassan, ya fitar ranar Litinin a Kaduna.
- Sojoji Sun Lalata Masana’antar Sarrafa Burodin ‘Yan Ta’adda A Borno
- Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara
“A ranar 4 ga watan Afrilu, jami’an ‘yansanda sun kama wani Alkali Danladi, mai shekaru 45, a kauyen Ungwan Hayatu, Yarkasuwa, a karamar hukumar Lere, a kan hanyar Kaduna zuwa Jos.”
Ya ce ana zargin Danladi da yi wa ‘yan bindiga safarar makamai kuma an kama shi ne a lokacin da ya taho daga Jos.
A cewarsa, a yayin bincike an gano inda Danladi ya boye wasu bindigu da suka hada da AK-47 guda daya, bindigu kirar gida guda biyar da kuma kananan bindigu guda biyu.
Ya kara da cewa, “An gano kayan aikata laifi da dama a wajensa da kuma layu na neman tsari,” in ji shi.
Ya ce binciken da aka yi ya kai ga kama wani Gayya Koddi mai shekaru 40 a kauyen Bundu Dingi.
Hassan ya ruwaito cewar kwamishinan ‘yansandan jihar, Ali Audu, ya tabbatar wa jama’ar jihar cewa rundunar na aiki tukuru don kama sauran wadanda ake zargi.
“Kwamishinan ya kuma bukaci mazauna yankin da su kasance masu lura tare da kuma kai rahoton duk wani abu ga jami’an tsaro,” in ji shi.