Rundunar ‘yansandan Jihar Yobe, ta kama wani matashi mai suna Sani Musa mai shekaru 22, wanda aka fi sani da Regis Oga Soja a unguwar Nawa Nawa Damaturu kan zargin daba wa wata ‘yar talla mai shekaru 24 wuka.Â
Matashin ya kuma kwace wayar ‘yar tallan.
- An Kira Taron Dandalin Tattaunawa Kan Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Faransa
- ‘Yan Kasuwar Afrika Sun Gano Zarafi Mai Kyau A Canton Fair
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.
Abdulkarim, ya ce an kama Musa ne tare da wayar ‘yar tallan kirar Itel A663LC/MTN a hannunsa.
DSP Dungus ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi.
Kwamishinan ‘yan sanda, Garba Ahmed, ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da adalci ba.
CP Garba ya kuma karfafa wa jami’an rundunar gwiwa da su ci gaba da tabbatar da doka da oda a jihar Yobe.
Ya kuma yaba wa al’ummar jihar kan goyon bayan da suke ba su na yaki da aikata laifuka a jihar.