Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa, ta hana wasu mutane biyu shigo da manyan makamai cikin jihar.
An kama su ne da misalin ƙarfe 3 na daren ranar 4 ga watan Yuni, 2025 a garin Lafia.
- Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Ya Yi Alkawarin Sulhu Da Takwaransa Na Arewa
- Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa bayan samun sahihin bayani, rundunar ta aike da jami’anta daga sashen yaƙi da garkuwa da mutane, inda suka cafke mutanen.
Ana zargin su da niyyar kai makaman zuwa Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Mutanen da aka kama su ne Lawal Sani, mai shekaru 40, direban mota daga ƙaramar hukumar Funtua a Jihar Katsina da kuma Dahiru Abdullahi, mai shekaru 75, dillalin shanu daga unguwar Angwan Dosa a Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna, wanda ɗan kasuwar shanu ne a Keffi da ke Nasarawa.
An kama su da manyan makamai ciki har da bindiga ƙirar GPMG, bindigu ƙirar AK-47 da sauransu.
Mutanen sun amsa laifin da ake zargin su, inda suka ce an biyasu Naira 500,000 domin su kai makaman daga Jihar Binuwsi zuwa Kwara.
Rundunar ‘yansandan ta ce da ba a kama su ba, makaman na iya shiga hannun ‘yan ta’adda.
Ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a wannan harkar safarar makamai.
Kwamishinan ‘yansandan, ya ce Nasarawa ba mafaka ba ce ga masu laifi, kuma za su ci gaba da yaƙi da masu safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma roƙi jama’a da su riƙa sanar da duk wani abin da suka gani mai kama da laifi, inda ya bayyana layukan gaggawa da za a iya kiran su: 08112692680, 08032564469, 08036157659, 08037461715, da 07032532391.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp