Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta kama wasu mutane 88 da ake zargi da aikata manyan laifuka guda 59 a jihar a cikin watan Fabrairu.
Kakakin rundunar ‘yansandan, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana haka a Katsina ranar Laraba.
- NiMet Ta Yi Hasashen Bullar Zazzabin Cizon Sauro A Watan Maris Da Afrilu
- Jakadun Kasa Da Kasa Dake Sin: Kuzarin Tattalin Arzikin Sin Zai Amfani Kasashen Duniya
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne bisa zarginsu da hannu a fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, da kuma kisan gilla da dai sauransu.
Ya ce ‘yansanda sun shigar da kararraki 49 a gaban kotuna kan wasu da aka kama.
Sadiq-Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami, 12 da laifin kisan kai, 19 da laifin fyade, uku da laifin yin garkuwa, yayin da sauran kuma aka kama su kan wasu laifuka.
Ya ci gaba da cewa, an kama mutanen uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wani samame na hadin gwiwa da rundunar ‘yansandan Katsina da babban birnin tarayya suka yi.
Kakakin rundunar ‘yansandan ya bayyana sunayensu da Hassan Ibrahim mai shekaru 25 da Ibrahim Ishaq mai shekaru 33 da Shafi’u Zubairu mai shekaru 30 duk a kauyen Kakabawa da ke Karamar Hukumar Kurfi ta jihar.
A cewarsa, yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata ta’addanci a kananan hukumomin Kurfi da Safana.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun ambaci wasu miyagun ‘yan bindiga guda uku da suke aiki da su, wadanda a yanzu suke hannun hukuma a jihar.
Sadiq-Aliyu ya kara da cewa an kama wani Bilyaminu Muhammad mai shekaru 32 a kauyen Zago da ke karamar hukumar Arewa ta Kebbi bisa laifin mallakar harsashi guda bakwai ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa, an ceto mutane 72 da aka yi garkuwa da su a fadin jihar a cikin watan Fabrairu tare da kwato dabbobi 500 da aka sace.