Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu da ake zarginsu da sace wasu kananan yara biyu tare da kubutar da yaran daga hannunsu.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Talata.
- NIS Ta Samar Da Fasfo Kimanin Miliyan 2 A Shekarar 2022 —Gwamnatin Tarayya
- Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci
Wadanda ake zargin sun hada da Nura Auwal mai shekaru 22 da ke unguwar Rijiyar Lemo a Kano da Abubakar Lawal mai shekaru 22 daga unguwar Bachirawa a Kano.
“A ranar 26 ga watan Janairu, mun samu labari daga Isyaku Salisu da Auwal Sale mazauna Bachirawa a Karamar Hukumar Ungogo a Kano, cewa an yi garkuwa da ‘ya’yansu Umar Isyaku mai shekaru 3 da Aliyu Auwal mai shekaru 4.
“An aika musu da sakon waya da bayanan asusun banki, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 20, amma daga baya suka biya Naira miliyan biyu kan kowane yaro.
“Da samun rahoton kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Mamman Dauda, ya umurci rundunar ‘Operation Restore Peace’ karkashin jagorancin SP Aliyu Auwal, jami’in da ke kula da masu garkuwa da mutane, sashen binciken manyan laifuka na jihar, da su kubutar da wadanda aka sace tare da kamo wadanda suka aikata laifin.
“An ceto wadanda abin ya shafa ba tare da sun ji rauni ba a wani gini da ba a kammala ba.”
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki ne suka yi garkuwa da yaran biyu tare da aika wa iyayensu sakon waya kan neman kudin fansa.
Kakakin ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.