Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, ta cafke wani da ake zargin barawo ne da ya sace wata tirela dauke da tan 35 na man gyada da darajarsa ta kai kimanin Naira miliyan 30.
Rundunar ta samu rahoton sace tirelar da aka ajiye a yankin Maraban Jos a Jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Afrilu, 2024.
- Harin Sojoji A Kauyen Sudan Ya Kashe Mutum 28
- Kasashen Ghana Da Kenya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa
Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce motar da aka sace mai lamba DAF CF 85, ta fito ne daga Umuahia a Jihar Abiya kuma tana kan hanyar zuwa Jihar Kano lokacin da ‘yansanda suka kama ta a Jihar Bauchi.
SP Wakil, ya ce bincike ya nuna cewa direban motar ya tsaya a Maraban Jos don yin wanka amma yana dawowa ya tarar an sace ta.
Kakakin ya ce rundunar ta samu damar kwato kaya masu yawa a cikin tirelar.
Wakil, ya kara da cewa an kama wanda ake zargin kuma an tsare shi domin yi masa tambayoyi.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Auwal Muhammad, ya bayar da umarnin gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar.
Rundunar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan ta kammala bincike.