Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wasu mutane biyu, Bawa Sa’idu mai shekaru 22 da Weti Saleh mai shekaru 25 a kauyen Jalingo da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade tare da jima ta rauni.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya ce jami’an hedikwatar ‘yansanda reshen Tarmuwa sun kama wadanda ake zargin ne a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 15:30 na rana.
Abdulkarim ya kara da cewa, wacce aka yi wa fyaden na samun kulawar gaggawa, yayin da aka mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Damaturu domin gudanar da bincike mai zurfi.