Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta kama wata mata ‘yar shekara 37 mai suna Fatima Abubakar bisa laifin azabtar da wata yarinya ‘yar shekara biyu da wani karamin yaro da ke hannunta saboda yin fitsari a kan gadonta.
‘Yansanda sun kama Fatima wadda ‘yar asalin garin Sanda ce a Unguwar Makama (B) ta Karamar Hukumar Yola ta Kudu a jihar bisa zargin azabtar da yaran saboda yin fitsari, da kuma yin bayan gida a daki.
- Kashi 67 Cikin 100 Na Ɗaliban Kaduna Sun Samu Nasara A WAEC – Kwamishinan Ilimi
- Wane Ne Ke Tallafa Wa Jam’iyyun Siyasar Nijeriya Da Kudade?
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje, wanda ya tabbatar da kamen, ya ce an kama mai laifin ne biyo bayan wani rahoto da wasu al’ummar yankin suka samu.
Matar wadda kuma kishiyar uwar yaran ce, ta wahal da su kuma ta amsa laifin da aka kama ta akai.
Nguroje ya ce makwabta sun ruwaito cewa matar ta saba azabtar da yaran tare da hana su abinci, inda ya kara da cewa wacce ake zargin ta gargade su da su daina tsoma baki cikin harkokinta.
Nguroje ya ce kwamishinan ‘yansandan jihar, Morris Dankombo, ya bayar da umarnin gurfanar da wacce ake tuhuma a gaban kotu domin ta girbi abin da ta shuka.