Rundunar ’Yansandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane da ake zargi da aikata fashi da makami, satar waya da kuma mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce jami’ansu sun kama shugaban wata ƙungiyar masu fashi da makami, Fahad Babangida, tare da abokan aikinsa a ranar 11 ga watan Satumba, yayin da suke shirin kai hari.
- Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
- Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin Kamfanoni Suna Gudanar Da Shawarwarin Kasuwanci Da Kyau Bisa Ka’idojin Kasuwa
Bayan haka, an kama ƙarin wasu mutane da suka ƙware wajen fasa shaguna da kuma waɗanda ke siyar da kayan sata.
An ƙwato wayoyi 45 da kwamfuta daga hannunsu.
A wani samame daban, jami’an ’yansanda sun kama wasu samari biyu da bindiga da harsashi a Unguwar Mu’azu, sannan kuma an cafke wani mai sayar da makamai, Simon Haruna, a Igabi da bindiga da harsasai.
Ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da su a kotu.
’Yansanda sun bayyana cewa kamen na cikin ƙoƙarin murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar Kaduna da kewaye.
Sun ƙara da cewa waɗanda aka kama sun amsa laifukansu, ciki har da fashi, satar waya da kuma sayar da kayan sata.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya jinjina wa jami’an saboda jajircewarsu wajen gudanar da aikin.
Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma, ya buƙaci ’yan kasa su kasance cikin shiri, tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama masu laifi.
Ya ce, “Idan muka haɗa kai, za mu tabbatar Kaduna ta kasance cikin zaman lafiya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp